Ku daina ganin laifin Shugaba Buhari- Obasanjo
– Rikicin Makiyaya da manoma: Ku daina ganin laifin Shugaba Buhari Inji Obasanjo
– Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo ya goyi bayan Shugaba Buhari
– Obasanjo ya sauran Gwamnoni da Shugabanni na Yankin
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo
Tsohon Shugaban Kasar nan Cif Olusegun Obasanjo ya goyi bayan Shugaba Buhari, Obasanjo yace Babu laifin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari wajen Rikicin Makiyaya da manoma da ake ta fama da shi a Kasar musamman yanzu da abin ya kara kamari.
Cif Olusegun Obasanjo yace abin na bata masa rai idan har ya ji Jama’a na kukan Makiyaya sun yi barna, Gwamnatin Tarayya ba tayi komai ba. Cif Olusegun Obasanjo yace wannan aikin Jihohi ne da kuma Kananan Hukumomi ba Gwamnatin Tarayyar Kasar nan ba.
KU KARANTA: Babu wasu shaidanu a fadar Villa
Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo yace har su Gwamnonin yankin ba su kyautawa. Yace sai ka ga Gwamna yana jiran Shugaban Kasa yayi maganin Makiyaya Fulani a Jihar sa. Obasanjo yace wannan ai aikin su ne ba na Shugaban Kasa ba. Yace wasu suna ganin ko dan Shugaba Buhari Bafullatani ne, hakan ya zama aikin sa.
Olusegun Obasanjo yace a shekarun baya akwai wuraren kiwon dabbobi a Kasar, yace sai dai yanzu bai san inda suka shige ba. Tsohon Shugaban Kasan yace ba daidai bane Makiyaya su auka gonar mutane suyi masu barna ba, yace yayi mamakin yadda ya ga sun mallaki manyan makamai. Cif Obasanjo yace gaskiya ya kamata Majalisa tayi wani abu game da wannan batu.
The post Ku daina ganin laifin Shugaba Buhari- Obasanjo appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.