Gwamnati ta bada Ranar Alhamis a matsayin hutu
– Gwamnatin Jihar Edo ta bada Ranar Alhamis a matsayin hutu a fadin Jihar
– Za a nada sabon Oba na Benin a wannan rana
– Babu zuwa aiki a Ranar Alhamis domin wannan gagarumin nadin sarauta
Gwamnan jihar Edo Adams Oshiomole
A Jihar Edo, an tabbatar da Ranar Alhamis mai zuwan nan a matsayin ranar hutu. Gwamnatin Jihar ta dauki wannan mataki ne saboda nadin sarautar sabon Oba na Benin da za ayi a wannan Rana.
A Ranar Alhamis dai babu zuwa aiki a kaf fadin Jihar, hakan zai ba Jama’a damar hallartar wannan gagarumin nadin Sarauta a Kasar. Ranar Alhamis dinnan 20 ga wata ne dai za a nada Yarima Eheneden Erediauwa kan kujerar sarauta.
KU KARANTA: Ka ga babban makiyin Shugaba Buhari
Farfesa Julius Ihonvbere, wanda shine Sakataren Gwamnatin Jihar na Edo ya bada wannan sanarwar, yace an bada wannan hutun ne domin nadin mai girma Eheneden. Tun farkon wannan watan dai aka fara shirye-shiryen nadin sarautar kamar yadda masu dillacin labarai suka rahoto.
Tarihi ya bada cewa an gina masarautar Benin ne tun karni na kusan goma sha daya, Oba Eweka shine Oba na Benin na farko, ya kuma yi sarauta daga shekarar 1180 har kusan shekarar 1300. Yanzu haka dai Sarki mai jiran gado yana wani wuri inda ake tsima sa domin karbar sarautar.
The post Gwamnati ta bada Ranar Alhamis a matsayin hutu appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.