Добавить новость
ru24.net
World News in Dutch
Октябрь
2016

Gwamnatin Buhari na taggayara ‘Yan Kasa- Kungiyar ASUU

0

Shugaban Kungiyar ASUU yace Gwamnatin Buhari ta tagayyara mutanen Najeriya

Shugaban ASUU yace bas u fa gane ma tsare-tsaren Gwamnatin ba

– Ya kira ‘yan Kasa da su tashi tsaye kan abin da duk suka ga zai cuta masu

Shugaban ASUU tare da Shugaba Buhari

Farfesa Biodun Ogunyemi wanda shine Shugaban Kungiyar ASUU ta Malaman Jami’a na Kasa ya koka da irin tsare-tsaren wannan Gwamnati. Farfesa Ogunyemi yace wannan Gwamnati ta wahalar da ‘Yan Kasar nan ta kuma taggayara su matuka.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Shugaban Kungiyar ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi yayi wannan bayani ne a Jiya yayin da yake zantawa da ‘Yan Jaridu.

KU KARANTA: An soke amfani da katin JAMB na shiga Jami’a

Shugaban Kungiyar ASUU yake cewa tsare-tsaren tattalin arziki da Gwamnatin ta kawo yana daga cikin abin da ke wahalar da ‘Yan Najeriya.

Shugaban Kungiyar ASUU, Farfesa Ogunyemi yace da farko Jama’a na bayan Gwamnatin kai da kwarkwata, sai dai bayan tafiya tayi tafiya, wasu suka fara cire rai ganin irin wahalar da ake ta fama da ita.

Farfesa Ogunyemi yace kamar fashi ne ace za a saida kadarorin Kasar nan, Farfesa Ogunyemi na ASUU yace matakan tattalin arzikin da Gwamnati ta dauka duk ba suyi daidai ba.

Farfesa Biodun Ogunyemi, Shugaban Kungiyar ASUU na Kasa ya kira ‘Yan KasaNajeriya da su tashi tsaye muddin suka ga wani tsari da zai cuta masu. Sai dai Tsohon Shugaban Kasa Cif Obasanjo yace mafi yawan abubuwan ba laifin Shugaba Buhari bane.

The post Gwamnatin Buhari na taggayara ‘Yan Kasa- Kungiyar ASUU appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.




Moscow.media
Частные объявления сегодня





Rss.plus
















Музыкальные новости




























Спорт в России и мире

Новости спорта


Новости тенниса