Boko Haram ta kai hari ta kuma sace wasu sojoji
Wasu rahotanni da dumi-duminsu ba cewa, ‘yan Boko Haram sun kai hari kan wani sansanin soji da ke wani kauye a arewa maso gabashin Najeriya a inda wasu sojojin sun bata, ake kuma zaton an sace su ne.
A wata sanarwa da rundunar sojin Najeriya ta fitar a ranar Laraba 19 ga watan Oktoba, ta ce, an kaddamar da wani yunkuri na gano inda wasu sojoji suka shiga, bayan da ‘yan Boko Haram suka kai hari a kan wani sansanin Soji da ke wani kauye a jihar Borno.
Harin ya zo ne a lokacin da wani bangare na ‘yan kungiyar suka saki ‘yan mata Chibok 21 daga cikin 200 da suka sace, ana kuma ana tattaunawa da gwamnati kan sakin sauran ‘yan matan 83 da ke hannu ‘yan ta’addan kimanin watannin 30 da suka wuce.
KU KARANTA KUMA: Sojojin Bangladesh sun jinjinawa na Nigeria
Kamfanin dillancin Labarai na Associated Press ya bada rahoton cewa, harin da aka kai Gagishar da ke kan iyakar Najeriya da Jamhuriyyar Nijar, na uku ke nan bayan tsagaita wutar da aka yi tsakanin gwamnati da mayakan na tsawon wata guda.
Kakakin Rundunar Soji, Kanar Usman Kuka Sheka, a sanarwar, ya kira harin da cewa, “wata karamar koma baya ne ga rundunar, daga burbushin ‘yan Boko Haram, ya tilastawa sojin ja da baya a shirin fada, kuma an kaddamar da wani gagarimin shiri na kokarin gano sojin da suka bace, da kuma fatattakar ‘yan ta’addan daga yankin baki dayansa”.
Ana kyautata zaton cewa, daya bangaren na ‘yan Boko Haram ne, da ta kira kanta da sunan “yankin daular Muslunci ta Afrika ta yamma” , da ba ta ga maciji da wacce ke karkashin Shekau, ta kai harin. Kungiyar wacce ta nadin sabon shugabanta a watan Agusta, ya janyo sa-toka-sa katsi da Shekau.
KU KARANTA KUMA: ‘Yan matan Chibok 100 ba za su dawo ba
Ana jin cewa, da bangaren da ke karakashin Shekau ne gwamnatin Swiss, da kuma kungiyar Red Cross, su ka shiga tsakani, tare da yin magana a madadin gwamnatin Najeriya, har aka sako ‘yan matan Chibok su 21 a ranar Alhamis da ta gabata.
Rikicin na Boko Haram da aka kwashe shekaru 7 ana yi, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 20,000, ya kuma tilastawa wasu kimanin miliyan 2 da 600,000 barin gidajensu, sannan ya kuma jefa dubun-dubata cikin hadarin yunwa a cewar kungiyoyin agaji na kasa da kasa da kuma Majalisar Dinkin Duniya.
The post Boko Haram ta kai hari ta kuma sace wasu sojoji appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.