Добавить новость
ru24.net
World News in Dutch
Октябрь
2016

Hadarin mota ya lakume ma’aikatan sharia’a su biyar

0

Mutuwa karan kwana, idan ajali yayi kira, sai an je.

A ranar talata 18 ga watan Oktoba ne wasu ma’aikatan fannin shari’a su biyar suka rasa rayukansu a wani hadarin mota a cikin garin Abuja, inda wasu muatne uku suka jikkata.

Mutanen sun fito daga ma’aikatun shari’a daban daban da suka hada da: Uku daga kwamitin koli na alkalai da lauyoyi, daya daga kotun daukaka kara, sai daya kuma daga kotun koli.

Jaridar Daily Trust ta bayyana hadarin ya faru ne tashar motar Mpape dake kan hanyar Kubwa yayin da suke jiran mota.

KU KARANTA: Sunayen wayoyin da zasu daina daukan WhatsApp

Wata shedar ganin da ido ta bayyana ma majiyar mu cewa wata direban mota dake amsa waya yayin da take tuki ne ta sauka daga kan hanya inda tayi kan mutanen, nan take suka mutu. Daga nan aka garzaya da sauran mutanen da suka jikkata zuwa asibiti.

Majiyar tamu ta bayyana mana cewa wani ma’aikacin kotun koli yace an kammala shirin binne musulman cikinsu.

The post Hadarin mota ya lakume ma’aikatan sharia’a su biyar appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.




Moscow.media
Частные объявления сегодня





Rss.plus
















Музыкальные новости




























Спорт в России и мире

Новости спорта


Новости тенниса