Gwamnonin Arewa 10 sun kai ziyarar aiki birnin Washington
Gwamnoni 10 daga cikin 19 dake Arewacin Najeriya sun kai wata ziyarar aiki don halartan taron kara ma juna sani da kwani 3 da kwalejin wanzar da zaman lafiya na kasar Amurka (USIP) ta shirya.
Gwamnonin Arewa
Kafar watsa labarai ta Sahara Reporters ta ruwaito cewa sakamakon gwamnonin suna gudun bakin jama’a kan yin tafiyan a daidai lokacin da tattalin arzikin kasar nan ke cikin mawuyacin hali, don haka ne suka bukaci mashirya taron dasu tabbatar al’ummar yankin Arewa sun amfana da wannan taro.
Yayin dayake gabatar da kasida a madadin gwamnonin, Gwamnan jihar Barno, Kashim Shettima yace gudanar da irin wannan tafiya a irin wannan lokacin da tattalin arzikin kasa ya tabarbare, sun san mutane zasu caccakesu, amma sun gwammace a caccakesu da suyi asarar rashin halartan wannan muhimmin taron saboda matukar amfanin da Arewa zata samu daga shi.
A yau Laraba 19 ga watan Oktoba ne aka kammala taron wanda ya samu halarcin Gwamnoni 10 da suka hada da Shettima (Borno), Aminu Tambuwal (Sokoto), Darius Ishaku (Taraba), Abdulfatah Ahmed (Kwara), AbdulAziz Yari (Zamfara), Bindo Jibrilla (Adamawa), Muhammad Abubakar (Bauchi), Abubakar Sani Bello (Niger).
KU KARANTA: Alkalai biyu sun sha tambayoyi a hannun hukumar EFCC
Sai kuma mataimakan gwamnoni da suka hada da:Farfesa Hafiz Abubakar (Kano), Farfesa Sonni Gwanle Tyoden (Plateau), Alh Wakkala( Zamfara), Martin Babale (Adamawa), da Usman Mamman Durkwa (Borno).
Shima ministan harkokin cikin gida Abdulrahman Dambazau ba’a barshi a baya ba, inda ya gabatar kasida a yayin gudanar da taron.
Ga sauran hotunan taron.
The post Gwamnonin Arewa 10 sun kai ziyarar aiki birnin Washington appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.