Добавить новость
ru24.net
World News in Dutch
Октябрь
2016

Shiri yayi! Za’a rika yi wa masu yi wa yara fyade a Indonesia ‘dandaka’

0

Shugaba Joko Widodo na Indonesia ya ce sabuwar dokar yin amfani da guba wajen yi wa duk wanda aka samu da laifin cin zarafin yara ta hanyar lalata dandaka, za ta rage yawan laifuka a kasar.

Shugaba Widodo ya gaya wa majiyar mu cewa Indonesia na mutunta hakkin dan adam da kundin tsarin mulki, amma fa idan aka zo kan batun laifin da ya shafi cin zarafi, gwamnati za ta dauki hukuncin ba sani ba sabo.

A farkon wannan watan nan ne, kasar ta yi dokar hukunta wadanda aka samu da laifin yi wa yara fyade taure (fidiya), ta hanyar amfani da guba, bayan gungun wasu bata-gari sun yi wa wata yarinya ‘yar shekara 14 fyade daga bisani kuma suka kashe ta.

KU KARANTA KUMA: An bukaci a soke wadannan muhimman hukumomin a jihohi

Kungiyar likitocin kasar ta Indonesia ta ce mambobinta ba za su shiga aiwatar da dokar ba domin ta saba ka’idojin aikin likita.

A wani labarin kuma A yau Laraba ne dan takaran Shugabancin kasar Amurka Donald Trump da Hillary Clinton ta Democrats za su sake karawa a muhawara tsakanin su karo na uku, kuma na karshe kafin babban zaben kasar a watan Gobe.

Za a tafka Muhawarar yau a jami’ar Nevada, Las Vegas, inda ake saran su kwashe awa daya da rabi suna fafatawa.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar iyayen matan Chibok sun fitar da wata sanarwa

Wani gogaggen dan jarida Fox News da ke Amurka Chris Wallace, mai shekaru 69, ne zai shugabanci muhawaran na ‘yan takara biyu.

Akalla mutane miliyan 84 aka kiyasta sun kalle Muharawan farko da aka gudanar ranar 26 ga watan Satumban da ya gabata.

The post Shiri yayi! Za’a rika yi wa masu yi wa yara fyade a Indonesia ‘dandaka’ appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.




Moscow.media
Частные объявления сегодня





Rss.plus
















Музыкальные новости




























Спорт в России и мире

Новости спорта


Новости тенниса