Добавить новость
ru24.net
World News in Dutch
Октябрь
2016

Sojojin Nigeria sun bata bayan arangama da yan Boko Haram

0

Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta ce wasu daga cikin sojojinta sun bace, bayan wani hari da aka kai masu a farkon wannan makon.

A wata sanarwa da kakakinta Kanar Sani Kukasheka Usman ya fitar, rundunar ta ce lamarin ya faru ne a yayin da wasu da ake zargi ‘yan Boko Haram ne suka kai hari a garin Gashigar, wanda ke kan iyaka da Nijar.

Yan kungiyar Boko Haram sun sace sojojin Najeriya tare da kai hari

Sanarwar ta kuma ce sojoji 13 ne suka jikkata a harin.

Rundunar ta kara da cewa an soma yunkurin gano inda sojojin suke, a yayin da ake ci gaba da kakkabe mayakan Boko Haram din daga yankin baki daya.

KU KARANTA KUMA: Kotun sojan Najeriya ta ladaftar da wani sojan ta

Sanarwar na zuwa ne bayan da wasu rahotannin da suka fito ta kafofin sada zumunta na intanet suka ce reshen kungiyar Boko Haram din da ke da alaka da kungiyar IS sun kashe sojojin Najeriya 20, kuma suka jikkata wasu da dama a wani hari da suka kai masu a arewa maso gabashin Najeriya.

Rahotannin sun ce ‘yan ta’addan sun fitar da wata sanarwa da ke cewa sun kai harin ne kan dakarun hadin gwiwar kasashen Najeriya da Nijar.

Tun da rikicin Boko Haram ya barke a arewa maso gabashin Najeriya dai, kungiyar ta kashe mutane sama da 20,000, a yayin da ta tilasta ma wasu sama da miliyan biyu da dubu dari bakwai barin muhallansu.

The post Sojojin Nigeria sun bata bayan arangama da yan Boko Haram appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.




Moscow.media
Частные объявления сегодня





Rss.plus
















Музыкальные новости




























Спорт в России и мире

Новости спорта


Новости тенниса