Gwamna Wike ya nunawa Buhari yatsa bisa wannan dalili
– Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers ce dalilin da ya hana DSS kama alakalin a jihar shi ne ba a bi ka’idar yin haka ba. – Wike ya kuma zargi gwamntin da kokari dakile ci gaban jihar da kuma kasha jam’iyyar PDP kuma ba za ta yi nasara ba – Gwamnan jihar ya kuma […]
The post Gwamna Wike ya nunawa Buhari yatsa bisa wannan dalili appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
– Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers ce dalilin da ya hana DSS kama alakalin a jihar shi ne ba a bi ka’idar yin haka ba.
– Wike ya kuma zargi gwamntin da kokari dakile ci gaban jihar da kuma kasha jam’iyyar PDP kuma ba za ta yi nasara ba
– Gwamnan jihar ya kuma ce da akwai shirye-shiryen makarkashiyar yin magudi a zaben cike gurbin da da za’a gudanar a jihar
![Wike](https://i.onthe.io/vllkyt5ntmrc2a8a2.aa477d37.jpg)
Gwamna Wike na jihar Rivers
Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike ya bayyana cewa, dalilin da yasa ya hana Hukumar jami’an tsaro na farin Kaya DSS kai sumame gidan wani alkali a jihar a tsakar daren 8 ga watan Oktobar 2016 shi ne ba a bi ka’ida ba.
A lokacin da ya ke jawabi a gidan gwamnatin jihar a Fatakwal a ranar Talata 18 ga watan Oktoba, gwamnan ya ce, ba ya yi haka bane domin hana Hukumar aikinta, sai dai don cewa ba a bi hanyoyin da suka kamata bana yin hakan.
Jaridar Vanguard ta rawaito gwamnan na zargin gwamnatin tarayya da kokarin murkushe jam’iyyarsa ta PDP, sai dai a cewarsa, a wani arashi, jam’iyya mai mulki ce da ke jan akalar gwamantin za ta mutu a siyasance.
KU KARANTA KUMA: Furucin Aisha: Buhari na cikin hadari a bisa wadannan dalilai
Gwamnan ya kuma yi ikirarin cewa, kokarin ‘yan barandan gwamnatin Buhari na dakile ci gaban jihar ba zai yi nasara ba, gwamna Wike ya kuma ce da akwai yunkurin magudin zaben da za a yi na cike gurbi a jihar, ya kuma yi gargadin cewa babu wanda ya isa ya yiwa jama’ar jihar fashin kuri’a duk da jami’an tsaron da za a jibge.
A wani labarin kuma mai shari’a John Inyang Okokro, daya daga cikin alkalan da Hukumar DSS ta kai sumame a gidansa, ya kuma rubuta wasika zuwa ga ministan shari’a Mahmud Mohammed, yana mai zargin cewa, an kai sumamen gidansa ne saboda ya ki ya taimakawa Rotimi Amaechi.
A cikin wasikar da ya rubutawa Baban Mai shari’a na kasa kuma kafar yada labarai na Sahara Reporters ta gani, Okoro ya ce, Dalar Amurka 38,000 da kuma Naira Miliyan 3 da 500,000 da Hukumar ta gano a gidajensa a daren Asabar 8 ga watan Oktoba, daga cikin alawus dinsa na hutu ne da kuma na ganin Likita ne da ka biya shi na shekaru uku.
The post Gwamna Wike ya nunawa Buhari yatsa bisa wannan dalili appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.