A maishe da Bautan kasa (NYSC) ganin dama ba wajibi ba – Shehu Sani ga FG
– An kashe wani mai bautan kasa a jihar Kaduna
– Sanata Shehu Sani wanda ke wakiltar Kaduna ta tsakiya yayi kira da ayi canji cikin aikin bautan kasa
– Yayi kira ga gwamnain tarayya ta sanya bautan ganin dam aba wajibi ba
National Youth Service Corps
Sanata Shehu Sani mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa ya shwarci gwamnatin tarayya da ta sanya bautan kasa ganin dam aba wajibi ba ko kuma a kara kudin kuma da inshore.
Ya fadi hakan ne bayan ya hadu da iyalan wani mai bautan kasan da aka kashe mai suna Lawal Kontagora wanda wasu yan bindiga suka kashe a Kaduna.
KU KARANTA: Yadda za a fita daga Matsalar Tattalin Arziki a Najeriya
Game da cewar News Agency of Nigeria (NAN), Lawal Kontagora na bautar kasan NYSC sa a Africdect information technology centre, Kaduna, kafin aka harbe shi a ranan 17 ga watan oktoba a unguwar Malali a jihar Kaduna.
Sanatan yace : “ wannan bas hi bane lokaci na farko ba, idan ya faru,muna Magana. Wannan ya faru a mazabata kuma wajibi ne in yin abinda zai yiwu.
“Idan irin wannan ya faru a wani wuri suka share,nib a zan yarda a. sai na kai wannan maganar majalisar dokoki; imam a mayar da shi ganin dama ko kuma a kara kudinsu ko kuma inshore.”
Mahaifin yaron, Alhaji Lawal Umar Kontagora,, ya nuna farin cikinsa da ta’aziyar da sanatan ya kawo musu.
“Sanatan mu ne kuma ya zo yi mana ta’aziyya, muna godiya. Ina addu’ za’ayi adalci saboda rasuwan yarona yayi mini zafi sosai”
Ofishin yan sanda jihar Kaduna sunce a damke mutane 3 da ake zargi tattare da kisan, kuma game da kakakin yan sanda ASP Aliyu Usman, yace an fara gudanar da bincike cikin al’amarin.
The post A maishe da Bautan kasa (NYSC) ganin dama ba wajibi ba – Shehu Sani ga FG appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.