Gwamnan jihar Kross Riba ya nada masu bada shawara 1,106
– Gwamnan jihar Kross Riba, Farfesa Ben Ayade yayi wani abin magana yayinda ya nada masu bashi shawara 1,106 a cikin wannan halin matsin tattalin arzikin da ake ciki
– Ayade yace yayi nadin ne saboda yaye talucin da ke jihar da ke da arzikin man fetur
Ben Ayade na Cross River
Gwamnan jihar Kross Riba, Farfesa Ben Ayade yayi wani abin magana yayinda ya nada masu bashi shawara 1,106 a cikin wannan halin matsin tattalin arzikin da ake ciki
Jaridar Punch ta bada rahoton cewa yayu nadin ne zuwa matsayoyi dabab-daban a ranan 25 ga watan oktoba. Matsayoyin sune, masu bada shawara, masu taimakawa na musamman, shugabanin ma’aikatu,da hukumomi.
KU KARANTA:Buhari ya bukaci yin kari cikin kasafin kudin 2016
Wannan sabon nadi da yayi a yanzu bayan ya nada kwamishananoni 28, masu bayar da shawara 65,da kuma fiye da mataimaka 109, da saura su.
Sabon nadin ya kunshi mutane 779 zuwa ma’aikatu, Hukumomi. 6 masu bada shawara, 30 manyan masu shawara, 75 mataimaka na musamman, 25 mataimaka na jiki.
Bugu da kari kuma akwai mataimaka 16 ga sarakunan gargajiya, wakilan kananan hukumomi 90, sakatarorin din din din 26, da sauran su.
Mai magana da yawun Ayade ,Christian Ita, wanda ya tabbatar da nadin yace zasu fara aiki ne daga 1 ga watan Nuwamba.
The post Gwamnan jihar Kross Riba ya nada masu bada shawara 1,106 appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.