Buhari ya cire shugaban ICPC Ekpo Ita
– Shugaba Buhari ya umurci shugaban ICPC ya tafi hutun dole
– A yau laraba ne Ekpo Ita zai fada ma ma’aikatansa cewa zai bar ma’aikatar
Ekpo Nta
Labarin da NAIJ.com ke samu yana nuna cewa an ce ma shugaban hukumar yaki da rashawa da kuma wasu laifuffuka , Ekpo Ita, ya tafi hutun dole.
Jaridar Vanguard ta bada rahoton cewa an ce Ita ya tafi hutun dole ne da sa ran cewa an kore shi kenan da wayau.
Rahotanni sun nuna cewa fadar shugaban kasa bata ji dadin yanda ICPC karkashin Ita ke gudanar da bincike akan manyan yan siyasa ba.
KU KARANTA:Bamu amince da nadin Jastis Binta a matsayin Alkaliyar karar Kanu ba – IPOB
Kana maaikatan hukumar yaki da rashawa suna kuka da yadda ake gudanar da shugabanci a hukumar wanda yake kawo rashin soyayya da kyawun aiki.
Rahoton ya nuna cewa wata wasika wacce ta fito daga ofishin sakataren gwamntin tarayya, Babachi Lawa, tace Ekpo Ita ya tafi hutun dole daga ranan 26 ga watan oktoba.
Game da cewar jaridar Vanguard ta bada rahoton cewa Nta ya fada ma shugaba Buhari cewa ai wa’adin shi zata kare ne 17 ga watan Nuwamba,2016, amma shugaba Buhari yace takardun da ke hannunsa ya nuna cewa yakamata ya bar ofishin ICPC 17 ga watan Nuwamba,2016.
Rahoton ya nuna cewa a yau laraba ne Ekpo Ita zai fada ma ma’aikatansa cewa zai bar ma’aikatar.
The post Buhari ya cire shugaban ICPC Ekpo Ita appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.