Abun mamaki! Gwamnan jihar Edo Adams Oshiomhole yayi jawabi mai girma
– Gwamnan jihar Edo Adams Oshiomhole ya bayyana cewa sabon gwamnan da aka zaba a jihar Godwin Obaseki ya fi shi iyawa
– Oshiomhole yace jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta fadi zaben jihar Edo da akayi kwanan nan saboda sun kasa tabbatar wa mazauna jihar iyawarsu
– Ya kuma ce tsawon lokaci da aikin gaskiya da yayi ga mutanen jihar Edo ji yaba APC karfi a kan jam’iyyar PDP
Godwin Obaseki na rawa kusa da Gwamna Adams Oshiomhole during campaign
Gwamnan jihar Edo Adams Oshiomhole ya bayyana cewa sabon gwamnan da aka zaba a jihar Godwin Obaseki ya fi shi iyawa, jaridar Daily post ta ruwaito.
Da yake Magana ga yan majalisa bayan taron jam’iyyar APC a Abuja, Oshiomhole yace yayi imani da cewa magajinsa zaiyi aiki sosai a matsayin gwamna.
KU KARANTA KUMA: Kudin makamai: ka bari kotu ta yanke hukunci- Fadar shugaban kasa ta sanar da Jonathan
Oshiomhole ya kuma ce jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ta fadi a zaben da aka kammala na jihar Edo saboda sun kasa tabbatar wa mazauna jihar iyawansu.
Gwamnan yace gaskiyarsa ga mutanen jihar Edo ne yaba jam’iyyar APC daman yin nasara a kan jam’iyyar PDP lokacin zabe.
A lokacin zaben jihar Edo da ya wuce, gwamnan da aka zaba a jihar yayi nasara mai tazara a kan dan takarar jam’iyyar PDP Osagie Ize-Iyamu.
A halin yanzu, za’ayi zaben gwamna a jihar Ondo a ranar Asabar, 26 ga watan Nuwamba.
Hukumar zabe ta kasa (INEC) tace zata tura ma’aikatan ta guda 16,723 domin su gudanar da zaben.
The post Abun mamaki! Gwamnan jihar Edo Adams Oshiomhole yayi jawabi mai girma appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.