Ana kokarin a hana bara a Najeriya
– Majalisar Dattawan Najeriya na yunkurin hana bara a Najeriya
– Wani Sanata daga Jihar Bauchi ya kawo wannan kudiri
– An koka da irin matsalolin da barar da ke kawo a Biranen Kasar nan
Majalisar Dattawan Najeriya na kokarin kawo wani kudirin haramta bara a fadin Kasar nan. Wani Sanatan APC daga Jihar Bauchi ya kawo wannan kudirin a Majalisa jiya. Wannan Sanata mai suna Isah Hamma Misau ya koka da halin da mabarata suke ciki da kuma bukatar a tsaida barar domin barnar da take kawowa.
A kudirin da ya saka wa suna ‘Illar bara da kuma bukatar tallafawa mabarata’ Sanata Isa Misau mai wakiltar Yankin Jihar Bauchi ta tsakiya, yace ana kokawa da matsalar barar a Kasar nan, musamman a manyan birane.
KU KARANTA: Ta sayar da jinjirar da ta haifa
Sanata Isa Hamma Misau yace ko da yake akan samu mabarata a ako ina a duniya, sai dai abin yayi yawa a Najeriya, sai ka ga mabarata a tasha, dakunan addini, kan tituna, wajen biki, da ma dai ko ina suna yawo a Kasar nan.
Mataimakin Majalisar Dattawar, Ike Ekweremadu wanda shi ya jagoranci zamar Majalisar yace ya kamata a duba wannan kudirin, Sanara Ekweremadu yace bai dace ace wasu al’adun na goyob bayan bar aba.
The post Ana kokarin a hana bara a Najeriya appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.