Mutane 3 sun rasa rayukansu yayinda rijiyan burtsatsi ta burma
–Mutane 3 ne suka rasa rayukansu a Onitsha jihar Anambra
–Mutanen sun mutu ne sanadiyar burmawa da su da rijiya tayi
– Biyu daga cikinsu yan jihar Akwa Ibom ne amma ba’a san sunayensu ba tukunna
Willie Obiano na Anambra
An samu wani tashin hankali a titin Hanik. Onitsha ,jihar anambra yayinda mutane 3 suka Burma rijiyan burtsatsi
Wani idon shaida ya bayyana ma jaridar Daily Sun cewa, rijiyan burtsatsin gargajiyan ya samu matsala ne sai wata mata ta gayyaci mutane suzo suyi mata gyara.
KU KARANTA:Ina da umurnin bincikar kowa da kowa – Shugaban EFCC
“Sun yi iwun neman taimako sai wani dan kalaba ya shiga domin ceto dan uwanshi,ashe shima ajalinshi kenan. Daga baya kuma wani bahaushe mazaunin unguwan yace zai shiga amma za’a biya shi N100,000 amma shima ya makale ciki.”
“Wani mutum mai rabo wanda ya shiga ciki amma ya fito da kyar fuskarsa duka a kumbure y ace aljanu sun mare shi.”
Jaridar Vangiard tace Dan sanda Mr. Apev yace an ciro gawawwakin su 3 kuma a sanar da hukuma akan abinda ya faru. Shi kuma mataimakin kwamishanan yan sandan , Yahaya Abubakar ya tabbatar da faruwan amma ana gudanar da bincike kan al’amarin.
The post Mutane 3 sun rasa rayukansu yayinda rijiyan burtsatsi ta burma appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.