Buhari ya gana da shuwagabannin kamfanin Shell
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da shuwagabannin kamfanin main a Shell a fadarsa inda yayi alkawarin zai maido da martaban aiki da gaskiya a gwamnatance.
Wannan ziyarar tasu tazo ne daidai lokacin da tsagerun Neja Delta suka dauki alhakin fasa bututun main a Escravos da safiyar ranar Talata 25 ga watan Oktoba, na matsayin gargadi ga gwamnatin Najeriya.
Wata sanarwar data samu sa hannun jami’i mai baiwa shugaban kasa shawara akan harkokin watsa labarai Garba Shehu tace shugaba Buhari zai yi iya bakin kokarinsa wajen ganin ya farfado shirin samar da ababen more rayuwa, musamman a bangaren samar da lantarki, tare da tabbatar da tsaro a yankin Neja Delta.
“Da haka ne kawai yan kasuwa zasu yi rigerigen shigowa kasar nan don zuba jari, wanda sakamakon hakan sai tattalin arzikin kasa ya habaka.” Inji sanarwar.
KU KARANTA: Yansanda sun dakile fashi a gidan man garin Owerri
Shima shugaba Buhari ya tabbatar ma kamfanin da cewa zai sama musu wutan lantarki, yace: “Zamu cigaba da baiwa tsaron kayayyakin samar da man fetur muhimmanci, tare da cigaban tattaunawa tsakanin al’ummar yankin da masu ruwa da tsaki.”
Daga nansai shugaba Buhari yayi kira ga kamfanin data mara ba mayakan rundunar sojan ruwa baya a yunkurinta na tabbatar da zaman lafiya a yankin Neja Delta.
A jawabinsa, daraktan kamfanin Mista Andrew Brown ya sanar da shugaba Buhari sake cigaba da fitar da danyen mai ta layin bututu na Forcardos bayan sun kammala gyaransa. Daga karshe sai ya bukaci da aka kara kaimi wajen samar da tsaro sakamakon sabbin kalubalen yan tsageru da suke fuskanta.
Brown ya yaba da kamun ludayin shugaban kasa Muhammadu Buhari musamman a fannin yaki da cin hanci da rashawa, sa’annan ya bayyana tabbacinsa na cewa tsarin farfado da tattalin arzkin kasar nan da shugaban ya dauko zai fitar da kasar daga kangin da take.
The post Buhari ya gana da shuwagabannin kamfanin Shell appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.