Muhimman labaran ranan litinin
Jaridar NAIJ.com ta tattaro muku muhimman labaran ranan litinin 31 ga watan Oktoba 2016.
1. Kishin-kishin tsige Oyegun daga karagar mulkin APC
Oyegun, Tinubu and Buhari
Kulle-kullen tsige Oyegun a matsayin shugaban jam’iyyar APC tayi kamari yayinda ake samun rahotannin cewa za’a nada shi a matsayin jakada
2. Bamu bukatan kudinka – Dattawan Neja delta ga Buhari
Masu ruwa da tsaki da kums dattawan Neja Delta sunce basu son aikin $10 billion (N4 trillion) da shugaba Buhari kr shirin musu. Wannan bayanin na fitowa ne yayinda dattawan yankin na shirin ganawa da shugaba Buhari a yau litinin , 31 ga watan oktoba a fadar shugaban kasa.
3. Boko Haram sun far ma sojin Operation Lafiya Dole
Wasu rundunar yan tada kayar bayan boko haram sun kashe jami’an sojin najeriya 9 a wata harin da aka kai. Sun kai harin ne a unguwar Talala da Aljigin a ranan lahadi, 30 ga watan Oktoba.
4. Kotun koli: Alkalan da ake zargi sun sauka daga kujerun su
Jaridar Punch ta bada rahoton cewa Alkalan, Wadanda ke cikin Wadanda ake bincike bayan harin da Hukumar DSS ta kai musu har gidajensu makonnin da suka gabata sun sauka daga kujerun da ganin damansu har sai an tsarkake su daga zargi.
5. Mutum 1 ya mutu sanadiyar zanga-zanga a Ondo
Olusegun Mimiko ya tafi Abuja kan rikicin Ondo
Zanga-zangan da akeyi a jihar Ondo sakamakon sauyin dan takaran da Hukumar INEC tayi ta zama doguwa, yayinda wani yaro dan makarantan sakandare ya rasa rayuwarsa a zanga-zangar.
6. Ina son Jonathan yayi mini shaida a kotu – Dasuki
Ana sa ran Goodluck Jonathan ya zo kotu domin yin shaida ga Sambo Dasuki bayan yacd bai yarda cewa Dasuki ya sace $2.2 billion badakalar kudin makamai
7.Fadar shugaban kasa na tabbatar ma ‘yan Najeriya game da ka’idojin Buhafi
Garba Shehu
Wata sanarwa daga babban mai baiwa shugaba Muhammadu Buhari shawara kan kafofin sadarwa da watsa labarai malam Garba Shehu na tabbatar ma ‘yan Najeriya cewa shugaban zai cigaba da rayuwarsa bisa ka’idojin da aka sanshi dasu.
8. Buhari zai kara da majalisar wakilai kan bashin $30 biliyan
Sabuwar takaddama na bullowa tsakanin bangaren zartaswa da majalisun tarayya kan bashin $29.96 biliyan da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ke niyyar ciwowa daga kasashen waje. Baya ga wannan bashin, ‘yan majalisar wakilai na nuna damuwarsu kan karin N180.8 biliyan da Bubari ke nema bisa ga kasafin kudin 2016.
9. Wani mutum ya watsa ma uwargidansa ruwan zafi
Matan mai suna Catherine Wakere,yar garin Kianamu village a Embu, kasar Kenya, na asibiti bayan maigidanta ya watsa mata ruwan zafi.
The post Muhimman labaran ranan litinin appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.