Wike dan baranda ne, ba gwamna ba – Amaechi
– Rotimi Amaechi yayi kira da magoya bayan APC kada su ja baya bisa ga barazanar Wike a zaben da za’a gabatar a jihar
– Ya kiraye su da kada suyi bacci kaman yadda masu zaben Amurka sukayi
– Ministan yace zaiyi fito na fito da duk wani barazanar Wike
Wike-and-Rotimi-Amaechi
Ministan Sufuri,Rotimi Amaechi yayi kira da magoya bayan APC kada su ja baya bisa ga barazanar Wike a zaben da za’a gabatar a jihar ribas da za’a gudanar a ranan 10 ga Disamba.
Jaridar the Nation ta bada rahoton cewa Amaechi yayi kira ga magoya bayansu vewa kada suyi bacci kamar yadda mutanen Amurka sukayi kuma ya lashin takobin fito na fito da duk wani barazanar da Wike zai yi.
KU KARANTA: Na kusa da Shugaba Buhari ba su san aiki ba-Sanatoci
Game da cewarsa, ko dame ko dan me, sai APC ta lashe zaben, kari da fewa ba zasu saki jiki da tsaro kamar yadda sukayi a zaben jiya ba.
Yayinda yake magana a kamfe na karamar Hukumar Gokana, kauyen mai takatan kujeran Sanata ,Magnus Abe,Amaechi yace Wike dan baranda ne wanda bai cancanci shugabanci ba.
Yace ba zai yarda APC tayi asaran wani kujeran majalisan dattijai ba, musamman garuruwan ogoni na Khana, Gokana, Eleme da Tai.
Amaechi yace : “Idan akwai wani garin da APC bata bukatan kamfe, Garin Ogoni ne, kuma Wike yace sai ci nan. Saboda haka ya manta nan. Yace zai turo abubuwa, duk abinda zai turo, mu ma zamu turo na mu.”
Ku biyo mu a shafin ta Tuwita @naijcomhausa
The post Wike dan baranda ne, ba gwamna ba – Amaechi appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.