2019: Ko Atiku zai iya kada Buhari?
– A Najeriya wasu har sun fara kada gangar siyasar 2019, yayin da wasu ke ganin lokaci bai yi ba tukunna
– Tun daga yanzu wasu magoya bayan tsohon Shugaban Najeriya kuma jigo a jam’iyyar APC, Atiku Abubakar (Turakin Adamawa) sun fara tuna ma ‘yan Najeriya cewa za su so gwaninsu ya yi takara a shekara ta 2019
An mai da bukin kaddamar da wata hanya a jahar Adamawa wata dama ta rada ma ‘yan Najeriya cewa Turaki fa na nan tafe a 2016. Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jahar Adamawa Alhaji Abdurrahman Abba Jimeta, ya ce lokaci ya wuce da mai kaza zai ci kai. Ya kara da cewa naka sai naka, Don haka su ‘yan Adamawa za su taka rawar gida.
Alhaji Abdurrahman ya kara da cewa idan ba don Turakin na Adamawa ba, da ba a yi siyasar da ta gabata ba. Ga masu gain Turaki ba zai kai labari ba, sai Abdurrahman ya ce daga zaben Trump na Amurka sun gane cewa Allah ne ki ba da mulki saboda kafin zaben an dauk sam Trump ba zai kai labari ba.
KARANTA KUMA: Sojojin Najeriya sun samu gagarumar Nasara
A wani labarin kuma, Jaridar Daily Trust tace Shugaba Buhari ya gana da Shugaban Majalisar Dattawa na Najeriya, Bukola Saraki a Ranar Jumu’a nan. Shugaba Buhari dai yayi ganawar sirri ne, daga shi sai Dr. Bukola Saraki a Ranar 11 ga Wata a Fadar sa.
Ganawar Shugaban Kasar da kuma Shugaban Majalisu na Kasar ya dauki kimanin sa’a guda. Bayan taron kuma Bukola Saraki bai bari yayi magana da ‘Yan Jarida da ke cikin Fadar Shugaban Kasar ba.
Ba a dade da Shugaban Kasar ya gana da Bukola Saraki ba, ya kuma gana tare da shi da Mataimakin sa, Ike Ekeremadu. Da alamu dai Fadar Shugaban Kasa na kokari dinke barakar da ke tsakanin ta Majalisar Kasar. Tashin farko dai Majalisa tayi facakalo da rokon Shugaban Kasar na aro kudi har Biliyan kusan $30.
Jaridar The Nation tace abin da aka tattauna ba zai wuce maganar karbo bashin da Gwamnatin Kasar ke kokarin yi ba. Sanatocin Kasar da dama suna kukan Shugaban Kasa ba yayi da su. Sau uku kenan Shugaban Kasar yana zama da Shugaba Majalisar Dattawar Kasar, Bukola Saraki.
The post 2019: Ko Atiku zai iya kada Buhari? appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.