‘Yan Kasuwa kabilar Igbo dake Lagos sunyi alkawarin ci gaba da bada goyon baya
– ‘Yan kasuwa kabilar Igbo dake Legas sun dauki alkawari ci gaba da goyon bayan ci gaban Legas da APC
– Sun bukaci jihar ta daina nuna masu banbanci
– APC ta yaba ma gudummuwar ‘yan kasuwan ta kuma yi masu alkawari mai armashi nan gaba
‘Yan kasuwa ‘yan kabilar Igbo dake Lagos sun ci alwashin ci gaba da goyon bayan ci gaban jihar, ta bukaci gwamnatin ta Kara yawan tuntubarsu domin kyakyawar fahimta.
KU KARANTA: Daga hawa: Sabon Gwamna ya canza tsari
NAN ta ruwaito ‘yan kasuwan wadanda suka taru kalkashin inuwar ‘yan kasuwa Igbo dake cikin APC sun bada sanarwar bayan taron da sukayi a Lagos inda sukayi kira da a daina abinda suka kira “banbancin da ake gwada ma ‘yan kasuwa Igbo ta hanyoyin haraji da tara a kasuwanni da yawa.”
Ku biyo mu a shafinmu ta Tuwita: @naijcomhausa
The post ‘Yan Kasuwa kabilar Igbo dake Lagos sunyi alkawarin ci gaba da bada goyon baya appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.