Buhari, Donald Trump zasu halarci binne Cif Offor
– Ana saka ran cewa Shugaban kasa Buhari da Trump zasu halarci binne Cif Bennett Offor
– Yaron marigayin ya gargadi masu laifi da kada su halarci garin da za’a binne shi
– Yayi alkawarin cewa manyan mutane daga ko’ina fadin duniya zasu hallara
Shugaban kasa Muhammadu Buhari da shugaban kasar Amurka mai jiran gado, Donald Trump zasu samu damar haduwa kuma akwai yuhuwar zasu tantance junansu idan suka hadu a gurin binne Cif Bennett Offor.
Wannan na cikin sanarwan da Cif Emeka Offor dan marigayin yayi a ranar Lahadi, 13 ga watan Nuwamba.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa dan kasuwar man daga Anambra yace za’a binne mahaifinsa a Oraifite wannan satin kuma ya gargadi masu yaga aljihu da sauran masu laifi da su tsere kamar yadda aka tanadi wadanda zasuyi maganinsu.
KU KARANTA KUMA: Boko Haram: kungiyar matasa sun shawarci sojojin Najeriya
Ya bayyana cewa ba zai yi kasa agwigwa gurin hukunta duk wanda zaiyi yunkurin tozarta abokansa da kuma manyan mutanen da zasu halarci jana’izan ba.
Mr. Tony Obi wanda shine mataimakin shugaban kungiyar binne Pa Benneth Offor ya bayyana shirye-shiryen binnewar a gidauniyar Emeka Okafor ya kuma ce shugabannin Afrika da dama zasu halarci taron.
Cif Offor yace: “Mahaifina ya yi aiki a hukumar yan sandan Najeriya na tsawon shekaru 35 sannan yayi ritaya, don haka bazamu bari kowa yazo nan ya bata mana bikin mutuwarsa ba, an tanadi jami’an tsaro don su magance yan iska.”
Ya bayyana cewa tsohon shugaban majalisar dattawa, Cif Ken Nnamani da kuma Senstor Anyim Pius Anyim zasu jagoranci yan majalisar dokoki zuwa gurin taron yayinda manyan mutane daga ko’ina a fadin duniya harda Trump zasu halarci taron.
The post Buhari, Donald Trump zasu halarci binne Cif Offor appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.