Buhari ya bada umurnin sallaman ma’aikatan gwamnati
– Gwamnatin tarayya tana shirin koran ma’aikata a hukumomin da ke karkashin ma’aikatar sufurin jirgin sama
– Ministan sufurin jirgin sama, Sanata Hadi Sirika yace hukumomin da abun zai shafa sune Federal Airports Authority of Nigeria (FAAN), Nigerian Airspace Management Agency (NAMA) and Nigerian Civil Aviation Authority (NCAA)
Senator Hadi Sirika
An samu rahotannin cewa Gwamnatin tarayya tana shirin koran ma’aikata a hukumomin da ke karkashin ma’aikatar sufurin jirgin sama.
Ministan sufurin jirgin sama, Sanata Hadi Sirika ya bayyana jakan ne a daren asabar, 12 ga watan Nuwamba a tarin mau ruwa da tsaki na sufurin sama a jihar legas.
KU KARANTA: Manyan ‘Yan PDP sun koma APC
Game da cewar Sahara Reporters, Sirika yayi bayanin cewa akalla akwai manyan manajoji 88 a sashen, kuma sunyi yawa fiye da yadda ake bukata.
Game da cewarsa, hukumumin da za’a sallami ma’aikata a cikinsu sune Federal Airports Authority of Nigeria (FAAN), Nigerian Airspace Management Agency (NAMA) and Nigerian Civil Aviation Authority (NCAA).
Ya bayar da tabbacin cewa gwamnati zata cigaba da sallaman ma’aikatan da ba’a bukata a ma’aikatar.
“A yanzu haka munada manajoji 88 a hukumokin. Bamu bukatan yawancinsu . yanzu haka an bamu umurnin yin sauyi a hukumokin. Mun fara da FAAN . ba da jimawa ba zamu je sauran ma’aikatun. Amma zamu yi hakan ne bisa ga doka”
Zaku tuna ceaa a ranan laraba, 12 ga watan oktoba an sallami manyan ma’aikata 21 a Hukumar sufurin jirgin sama (FAAN).
Ku biyo mu a shafin ta Tuwita: @naijhausacom
The post Buhari ya bada umurnin sallaman ma’aikatan gwamnati appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.