Darajar Naira na kara karfi bayan an dauki wani mataki
– Bayan an kama ‘Yan Canji, darajar Naira na ta kara karfi a kasuwa da kuma Babban Bankin CBN ya gana da ‘Yan Canji
– Ana kokarin ganin yadda Darajar Naira za ta dan tashi
Darajar farashin Naira ta samu tashi a kasuwar canjin kudi na Najeriya bayan an dauki wani mataki a wancan makon. Darajar Naira na Najeriya ya samu dagawa sama ne a dalilin kama ‘Yan canjin kudi da Hukumar DSS masu fararen kaya suka yi. Hukumar DSS ta kama masu sayar da dalar da shegen tsada.
Jami’an Hukumar DSS sun kama ‘Yan Canji da ke manyan Birane irin su Lagos da Abuja. Jami’an farar hular sun ce ‘Yan canjin su saye dala a kan N390 sannan su sayar a kan N400 kowace Dalar Amurka guda. An yi haka ne don kara darajar dalar a kasuwar canji. A kwanakin baya an canza N465 kan kowace Dalar Amurka guda, yanzu kuwa ana saida Dalar ne a kan N400.
KU KARANTA: Nawa aka ba Yan Boko Haram na matan Chibok?
Babban Bankin Kasar na CBN ya gana da wadanda abin ya shafa domin ganin an rage wannan matsala. CBN na bada dalar Amurka ta Travelex kan N385. Hakan ta sa sauran ‘Yan kasuwa suka fara sayar da dalar kan N385 zuwa N400 kamar yadda aka yi yarjejeniya.
Babban Bankin Kasar na CBN ta bada umarnin ka da wanda ya kara fiye da kashi 2% na riba wajen sayar da dalar. Don haka ne aka yi amfani da Jami’an tsaro masu fararen kaya.
Ku biyo mu a shafinmu ta Tiwuta: @naijcomhausa
The post Darajar Naira na kara karfi bayan an dauki wani mataki appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.