Muhimman abubuwan da suka wakana a karshen mako
Jaridar NAIJ.com tattaro muku muhimman abubuwan da suka wakana a karshen makon da ya gabata
1. Kuma dai: Shugaba Buhari ya kara ganawa da Bukola Saraki
Jaridar Daily Trust tace Shugaba Buhari ya gana da Shugaban Majalisar Dattawa na Najeriya, Bukola Saraki a Ranar Jumu’a nan. Shugaba Buhari dai yayi ganawar sirri ne, daga shi sai Dr. Bukola Saraki a Ranar 11 ga Wata a Fadar sa.
2. Ka ji masu neman Atiku Abubakar ya tsaya takara 2019
Mutanen Adamawa sun ce su fa suna bayan Alhaji Atiku Abubakar idan zai tsaya takarar Shugaban Kasar nan. Gwamnatin Jihar tace tana bayan Atiku Abubakar dari-bisa-dari wajen ganin ya zama Shugaban Kasar Najeriya.
3. Jihar Edo: An yi sabon gwamna
A jiya Asabar aka nada Sabon Gwamna a Jihar Edo. Mista Godwin N. Obaseki ya zama Sabon Gwamna na Jihar bayan wa’adin Tsohon Gwamna Adams Oshiomole ya kare. Gwamna Obaseki ya yabawa Kwamared Adams Oshiomole da irin ayyukan da ya zuba a Jihar.
4. ‘Yan Boko Haram fiye da 200 sun sallama
Rahotanni na nuna cewa Mayakan Boko Haram sun mika kawunan su da iyalan su, sun kuma ajiye makaman Yaki. ‘Yan Boko Haram din sun mika kan su ne a Kasar Chad cikin wata daya zuwa biyu da suka wuce.
5. Tashin Hankali: Bam ya kashe wani gwamna
shugaban kasar turkiyya
Harin bam yayi sanadiyar mutuwar wani Gwamna a Kasar Turkiyya. Wannan mummunan abu ya faru ne a kwanan nan. Tuni dai Jami’an ‘Yan Sanda suka kama wadanda ake zargi har mutane 30. ‘Yan ta’addan sun tada bam din ne a Ofishin Gwamnan, hakan yayi sandaiyar mutuwar sa da wasu mutanen.
6. An hallaka dansanda a jihar Nassarawa
A cewar kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Abubakar Sadik Bello wanda kuma ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar jumaa 11, Nuwamba, ya kuma ce, lamarin ya faru ne a lokacin da ‘yan sanda ke sintiri a kan hanyar obi zuwa Agwatashi a kimanin makonni biyu da suka gabata.
The post Muhimman abubuwan da suka wakana a karshen mako appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.