Manyan ‘Yan PDP sun koma APC
– A zaben jihar Ondo, wasu manyan ‘yan PDP irin su Elegbeleye sun bar Jam’iyyar PDP sun koma APC
– Fiye da mutane 5000 suka sauya sheka daga PDP zuwa APC
– Elegbeleye ya kira mutanen sa da su zabi Rotimi Akeredolu na APC a matsayin gwamna
Wani daga cikin Manyan ‘yan PDP na Jihar Ondo, Gbenga Elegbeleye ya bar Jam’iyyar ta PDP, ya koma APC yayin da bai wuce saura mako biyu ayi zabe ba. A Ranar 26 ga wannan Wata ake sa ran cewa za a zabi sabon Gwamna a Jihar Ondo.
Gbenga Elegbeleye bai dade daga sauka daga matsayin Shugaban NSC na wasanni ba, ya tabbatar da cewa ya bar Jam’iyyar PDP ya koma Jam’iyyar APC mai adawa a Jihar. Jarida Leadership tace Tsohon Shugaban Hukumar Wasannin na Kasa ya tattara da mutanen sa fiye da 5000, sun bar Jam’iyya ta PDP.
KU KARANTA: Muna bayan Atiku – Inji Gwamnatin Adamawa
Daga cikin mutanen Elegbeleye da suka fice daga PDP zuwa APC akwai; Ojo Victor, Thompson Otitio Atikase, Muyiwa Asangula dsr. Ojo ya taba rike Shugaban Karamar Hukuma, Muyiwa kuma ya taba zama mai ba Gwamna Mimiko shawara, shi kuma Thompson Atikase, tsohon Dan Majalisar Jihar ne.
Mista Gbenga Elegbeleye yayi kokarin fitowa takara a PDP, ko da ya rasa, sai ya koma Jam’iyyar APC, inda yace yana bayan Dan takara Rotimi Akeodolu na APC. Gbenga Elegbeleye yace Gwamna Mimiko bai tsinana komai ba, yace amma kuwa, Rotimi Akeodolu zai yi masu tituna a Garin su.
The post Manyan ‘Yan PDP sun koma APC appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.