Ya kashe yarinyar budurwarsa da duka
Wani dan saurayi mai shekaru 22 mai suna Uriel Vega dan asalin jihar Chicago na kasar Amurka ya shiga komar yansanda a ranar Talata 8 ga watan Nuwamba inda ake zarginsa da laifin aikata kisan kai.
Uriel Vega
Shidai Uriel ana tuhumarsa ne da laifin kisan kai bayan yayi ta dukan wata jaririya mai suna Raiylana Vasquez yarinyar budurwarsa yayin da yake yin rainonta a gida. Jin haka ya sanya makwabta kiran yansanda, sai dai ko kafin su zo yarinyar ta jigata, kuma an ga alamun shaidan duka a jikinta.
KU KARANTA:Anyi ma magidanci tonan silili kan satar tukunyar miya
Lauyan mai kara yace banda ma duka da yarinyar ta sha a hannun Uriel Vega, har taka ruwan cikinta yayi, likitoci a asibitin Holy Cross ne suka bayyana mutuwar jaririya Raiylana. Sai dai bincike ya nuna cewar jaririyar ta mutu ne sakamakon wahalar da ta sha a hannun Vega.
Zuwa yanzu dai Vega na hannun hukuma, kuma bashi da wakilci na lauya kowane iri, sai dai haryanzu yansanda basu bayyana dalilin daya sanya Vega kashe jaririuar ba.
Fatan mu a nan shine, Allah ya shiga tsakanin nagari da mugu
The post Ya kashe yarinyar budurwarsa da duka appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.