Shekau ya nunawa sabon shugaban Amurka yatsa
-Shugaban ‘yan kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya mayar da martani kan zaben Donald Trump a matsayin shuagaban Amurka
-Shekau ya ce shi da mabiyansa na kan bakansu kuma shege ka fasa shi da sabon shugaban
Shuagan Boko Haram ya ce, Shege ka fasa tsakanin shi da Trump
Abubakar Shekau, shugaban kungiyar ta’addan Boko Haram ya mayar da martani kan zaben Donald Trump a matsayin sabon shugaban Amurka.
A wani sako na sauti da ya aika shafin intanet na Youtube a daren Lahadi 13 ga watan Nuwamba, Shekau ya ce, “Trump ba zai razana su ba, ko kuma duk wani wanda ke cikin kungiyar taron dangin da ke yakar ‘yan uwa da ke Syriya, da Iraqi, da Afghanistan da ma ko ina a duniya.”
Jaridar Punch ta rawaito cewa, “shugaban kungiyar Boko Haram wanda ya yi jawabin nasa a harshen Hausa, na cewa, yaki yanzu muka fara, mun ga bayan Obama, yanzu kuma za mu fara da Trump. Muna nan kan bakanmu ba kuma za mu daina ba.”
Duk da cewa kungiyar IS da Boko Haram ke yiwa mubayi’a a watan Agusta ta ce ta sauya Shekau da Abu Mus’ab Al Barnawi, dan marigayi Muhammadu Yusuf wanda ya kirkiro kungiyar, har yanzu Shekau na ikirarin shugabancin kungiyar.
KU KARANTA KUMA: Shekau ya mayar da martani ga nadin sabon shugaba
Wata guda ke nan kungiyar ta’addar ta sako ‘yan matan Chibok su 21 daga cikin sama da 200 da ta sace daga makarantara sakandaire ta Chibok, bayan cimma wata yarjejeniya da gwamnati.
Sama da 20,000 ne suka mutu yayin da wasu kimanin miliyan 2 da 600,000 suka rasa muhallinsu tun she karr 2009 a lokacin da Shekatu ya zama shaugaban kungiyar.
A yakin neman zabensa, shugabamai jiran gado na Amurka Donald Trump ya yi alkawarin ganin bayan kungiyar IS ba ta da bata lokaci ba da zaran ya hau karagar mulkin kasar
The post Shekau ya nunawa sabon shugaban Amurka yatsa appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.