LABARI MAI DADI: Yan Najeriya 490,000 zasu samu ayyukan yi a sabon shirin buhari
– Chris Ngige ya bayyana cewa za’a samar da ayyukan yi kusan rabin miliyan nan bada jimawa ba
– Ministan yace hakan zata samu ne ta hanyar dandamalin manoma masu hazaka ( Smart Farmers ICT)
– Ya kuma ce gwamnati ta mayar da hankali a kan sarrafa tattalin arziki
Sanata Chris Ngige ya bayyana cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari zata samar da ayyukan yi guda 490,000 ta hanyar dandamalin manoma masu hazaka da ta kaddamar kwanan nan.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa ministan aiki da daukar ma’aikata ya bayyana hakan a cikin karshen mako a taron kasuwaci na kasa-da-kasa na 30 da akayi a Lagas mai taken “daidaita tattalin arziki don daidaita dorewarsa da kuma bunkasa su”.
KU KARANTA KUMA: An jefa Osinbajo cikin duhu a Minna
Ngige yace gwamnati ta mayar da hankali gurin shafe rashin aiki ta hanayr samar da ayyuka ya kuma bukaci mutane da suyi kyakkyawan zato kan wannan yunkurin.
Ministan ya bayyana cewa ma’aikatar ta kaddamar da dandamalin manoma masu himma ( Smart Farmers ICT) don ci gaba da kuma kara yawan samar da kayayyakin noma a Abuja.
Ya ce: “kafin a gano mai a Najeriya, tattalin arziki ta dogara kan aikin noma. A lokacin yancin kai, aikin noma ta lashe kaso 70 cikin 100 na albarkatun kasa. Shekaru 25 bayan yancin kai, mu fuskanci wani mummunan kalubale tare da kayayyakin abinci wanda ya nuna cewa sama da kaso 50 cikin dari na kayayyain abinci ana shigo da su ne. idan mukace mu riki noma a matsayin abu na farko, sarrafa tattalin arziki zai zama mai dorewa, mun tabbatar da laifinmu.”
Mista Olakunle Obayan wanda ya kasance darakta-janar na daukar ma’aikata na kasa ya ce gwamnati ta mayar da hankali gurin janyewa daga dogaro a kan mai da gas zuwa ga sauran sassa.
The post LABARI MAI DADI: Yan Najeriya 490,000 zasu samu ayyukan yi a sabon shirin buhari appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.