‘Yan bindiga su yanke kawuna wasu yara 3 a Taraba
-Wasu yara uku sun gamu da ajalinsu a hannun wasu da ake zargi ‘yan bindiga ne a yayinda suke wasa a wata korama a jihar Taraba
-‘Yan bindiga sun hallaka yaran sun kuma yanke kawunansu a ciki wani hali na rashin imani
– Matar gwamnan jihar ta jajajantawa iyalan yaran tare da yin Allah Wadai da wannan mummunan kisa na wadanda ba su da laifin kowa
Wasu ‘yan bindiga sun hallaka wasu yara su uku ‘yan gida daya, tare da yanke kawunansu a jihar Taraba.
Yaran wadanda ba’a bayyana sunayensu ba, an harbesu ne da bindiga kafin a yanke kawunansu a cikin wai yanayi na rashin imani da tausayi a Dissol da ke karamar hukumar Gassol ta jihar Taraba a ranar Litinin 7 ga watan Nuwamba.
A cewar jaridar National Mirror, yaran duk ‘yan gida daya ne a kuma lamarin ya zama abin bakin ciki, da takaici, da kuma jimami a cikin garin da lamarin ya faru.
KU KARANTA KUMA: An hallaka dansanda a Nassarawa
A cewar wani shugaban addinin Kirista na yankin, Rabaran Fada Julius Ioryue, a hirarsa da ‘yan jaridu a Jalingo babban birnin jihar ya ce, yaran suna wasa ne wata korama a kuma bainar jama’a, aka harbesu, ya kuma ce ‘yan bindigar na dauke da muggan makamai masu hatsari, a inda suka hallaka ‘ya ‘ya uku daga cikin hudu na Mista James Agambuegh da matarsa mazauna garin.
Jaridar ta kuma rawaito cewa, Barrista Anna, matar gwamna Darius Isiyaku na jihar, ta je ta’aziya ga iyayen yaran, ta yi Allah wadai da wannan rashin imani, ta yi kuma kira ga jama’a da su zauna lafiya da junansu, sannan ta kuma yi alkawarin mika maganar gaba domin hukumomin da ya kamata su dauki matakin da ya dace kan faruwar lamarin.
Jihar Taraba na daya daga cikin jihohin da ke fama da rikice-rikice masu nasaba da addini kuma kabilanci, kawo yanzu ba’a san wadanda suka aikata kisan yaran ba, da kuma dalilin aikata kisan.
Ku biyo mu a shafinmu na Tuwita: @naijcomhausa
The post ‘Yan bindiga su yanke kawuna wasu yara 3 a Taraba appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.