Donald Trump zai fitad da mutane million 3 daga Amurka
Donald Trump yace zai kore mutane miliyan 3 ko kuma ya tsare su da kuma kana yace zai gina bango tsakanin Amurka da Mexico
Shugaban kasan Amurka mai jiran gado, Donald Trump yace zai kore masu hijra 3 million daga cikin Amurka idan ya hau mulki.
Trump ya bayyana hakan ne a wata hiran tasha CBC na farko bayan nasararsa a zaben kasar Amurka da y aba mutane mamaki.
Game da cewar sa, wadanda za’a kora suka yan hijra masu laifi irinsu yan daba da kuma masu hulda ga kwayoyi.
KU KARANTA: An sake gano wasu kudade $175m dangane ga Patience Jonathan
Trump yace domin yin haka, sai an hada da wasu yan tsirarun da gwamnati ke sane da su amma suna da laifi.
Trump yace: “Abninda zamuyi shine mutanen da ke da tarihin laifi, yan daba, yan kwaya, kimanin 2 million, ko ma 3 million, zamu fitad dasu daga kasar mu ko kuma mu tsare su.”
Shugaban kasan Amurka mai jiran gado, Donald Trump bai yi Magana akan miliyoyin mazauna kasar Amurkan wadanda gwamnati bata san da zaman su ba kimanin 10 million.
Ku biyo mu a shafinmu ta Tuwita: @naijcomhausa
The post Donald Trump zai fitad da mutane million 3 daga Amurka appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.