Kishi: An yi amarya wanka da ruwan acid
– Mista Chidi Ubochiadinjo ya shirya kara aure a watan Disamba
– Uwargidarsa Mrs Nkeiru Chidi Ubochiadinjo bata amince ba kuma tace zata dau mataki
Wata budurwa mai suna, Ogochukwu Nwosu, anyi mata wanka da ruwan acid bayan ta amince da auren wanni mutum.
Game da rahoton da muka samu daga NAIJ.com Gossip , wani mutumi ami suna Mr Chidi Ubochiadinjo ya nemi Miss Ogochukwu. Da farko ta ki amincewa da auren saboda ta san yanada aure, amma daga mutumin ya nace, sai ta amince da cewa zata aure shi. Amma sunyi yarjejeniyar ya fada ma uwargidanshi abinda yake niyyan yi.
KU KARANTA:Wike dan baranda ne, ba gwamna ba – Amaechi
Wannan abun ne ya batawa uwargidan Mr Chidi rai, mai suna Mrs Nkeiru Chidi Ubochiadinjo,ta fara kiran Miss Ogochkuwu tana yi mata barazana ta wayan sadarwa, tace mata kafin Disamba ta za’a daura auren, sai ta cutar da ita. Miss Ogochukwu ta fada ma mijin abinda matarsa keyi mata na barazana. Mijin yace kada ta damu kuma kada ta kai kara ofishin yan sanda.
A ranan 6 ga watan oktoba, yayinda Miss Ogochkwu take dawwa daga wajen aiki mialin karfe 8 na dare, wani mutum a sauka daka babur ya watsa mata ruwan acid.
Ku biyo shafinmu ta Tuwita: @naijcomhausa
The post Kishi: An yi amarya wanka da ruwan acid appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.