Sabuwa : An kashe mutane 2 a jihar Edo a zanga-zanga
Daliban jami’ar Ambrose Ali University sun rasa rayukansu da kuma suna zanga-zanga ne akan karin kudin makaranta
Akalla daliban jami’ar Ambrose Ali University da ke Ekpoma jihar Edo sun rasa rayukansu yayinda aka harbe su a wata zanga-zanga a yau, litinin 14 ga watan Nuwamba.
Jaridar Eagle online ta bada rahoton cewa daliban na zanga-zanga ne akan Karin kudin makaranta da shugabncin jami’ar tayi kawai sai aka harbe su.
KU KARANTA: Aljannar duniya! Hotuna 13 na kayataccen gidan Donald Trump da zai lula da kai duniyar tunani
Daliban dai ana sa ran cewa sojojin da aka tura wajen ne suka harbe su. An ce sojojin sunyi harbi sama ne domin watsa taron amma wasu harsasai suka kubuce wanda ya sabbaba rasa rayukan daliban guda 2.
Har yanzu dai babu jami’in da ya tabbatar wannan faruwan.
The post Sabuwa : An kashe mutane 2 a jihar Edo a zanga-zanga appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.