Real Madrid na kan hanyar kafa wannan muhimmin tarihin
– Real Madrid ta yi wasa 28 a jere ba tare da an doke ta ba a dukkan fafatawar da ta yi tun daga kakar bara zuwa bana
– Madrid a karkashin jagorancin Zinedine Zidane ta fara da doke Eibar 4-0 a ranar 9 ga watan Afirilun 2016, daga nan ta ci wasa 9 jumulla daga 11 da ta yi daga nan ta lashe kofin zakarun Turai na 11 a Milan.
Ronaldo celebrates his goal against Bilbao last term
Real Madrid ta fara da lashe UEFA Super Cup a kakar bana, kuma a kakar shekarar nan ta yi wasa 17 ta lashe guda 12 ta yi canjaras a fafatawa biyar, sannan tana mataki na daya a kan teburin La Liga.
Jumulla Madrid ta yi wata takwas ba ci ta a wasa ba a jere ta samu nasara a karawa 21 da kuma yi canjaras a wasa bakwai.
KU KARANTA: Ta kara kwabe wa Messi da kasar sa Argentina
Hakan na nufin kungiyar ta yi gumurzu sau 18 a gasar La Ligar Spaniya, sannan ta yi guda takwas a gasar cin kofin Zakarun Turai, ta kuma buga sauran wasannin a Copa del Rey da UEFA Super Cup.
A wani labarin kuma, Dan wasan tawagar kwallon kafa ta Wales, Gareth Bale, ya ce suna da kwarin gwiwar cewar za su samu tikitin shiga gasar cin kofin duniya duk da kunnan doki 1-1 da suka tashi da Serbia a ranar Asabar.
Kasashen biyu sun fafata ne a wasan shiga gasar cin kofin duniya, inda Bale ya fara ci wa Wales kwallo daga baya Aleksandar Mitrovic ya farke ta da ka.
Da wannan sakamakon Wales tana mataki na uku a kan teburin rukuni na hudu, inda Jamhuriyar Ireland wadda ke mataki ta ba ta tazarar maki hudu, za kuma su fafata a tsakaninsu a Dublin a ranar 24 ga watan Maris.
Wasan da Wales ta yi a ranar Asabar a filinta da ke Cardiff shi ne na uku da tawagar ta yi canjaras a fafatawa uku a jere, kuma ita ce ke fara cin kwallo daga baya a farke.
The post Real Madrid na kan hanyar kafa wannan muhimmin tarihin appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.