Dalilin da yasa muke kai sabbin hare-hare -Tsagerun Neja Delta
-Tsagerun yankin Neja-Delta a Najeriya, sun bayyana cewa mamaye yankin su da sojan kasar suka yi na barazana ga tattaunawan sulhu, kuma shine ummal-habaisin sake kai munanan hare-haren kan bututun mai da fasa bututun dake yankunan su
-Tsagerun na Niger Delta Avengers, NDA sun fadi a shafin su ta yanar gizo cewa kada a zarge su da wani laifi saboda fasa bututun danyen mai dake yankin nasu ganin yadda Gwamnati ke kara jibge masu sojoji dake barazana ga mazauna yankin
The Niger Delta Avengers have blown up escravos pipeline
Kalaman ‘yan tsageran na zuwa ne kwanaki kadan bayan da suka kai wani kazamin hari inda suka Burma bututun danyen mai na Trans Forcados Pipeline.
A wani labarin ma, Kungiyar Tsagerun Najeriya da ake kira Neja Delta Avengers sun dauki alhakin kai hari tashar fitar da danyan man fetur din kasar zuwa kasuwannin duniya mallakar kamfanin Shell.
KU KARANTA: Tsagerun Neja Delta sun fasa bututun mai
Mai Magana da yawun kungiyar, ya sanar ta kafar sadarwar twitter cewar, su suka fasa bututun man.
Rahotanni sun tabbatar da fasa bututun ranar talata, wanda ake ganin babbar koma baya ne ga yunkurin gwamnatin kasar na sasantawa da mutanen Yankin Neja Delta.
A satin da ya gabata ne dai NAIJ.com ta ruwato cewa A Najeriya, kamfanin mai na Shell, ya ce ya rufe tashar samar da iskar gas ta Escravos da ke yankin Neja Delta mai azrikin man fetur.
Sanarwar na zuwa ne sakamakon zanga-zangar da wasu mazauna yankin suka yi a ranar Laraba.
A cikin wani sakon email da ya aikewa manema labarai, kamfanin na Shell din ya ce zai cigaba da ayyukansa a Escravos din idan masu zanga-zangar sun watse.
Masu zanga zangar sun kwashe kwanaki takwas suna gudanarwa, inda suka yi korafin rashin ababem more rayuwa a yankin.
The post Dalilin da yasa muke kai sabbin hare-hare -Tsagerun Neja Delta appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.