Добавить новость
ru24.net
World News in Dutch
Ноябрь
2016

Labari da dumi duminsa: Sarkin Musulmi mai murabus ya rasu (Hotuna)

0

– Mahaifin Sambo Dasuki da kuma Sarkin Musulmi mai murabus mai suna mai martaba Ibrahim Dasuki ya rasa ransa a Litinin, 14 ga watan Nuwamba 

– Wani tsohon Sarki da tsohon shugaban soja Janar Sani Abacha ya kori ya rasu a wani Asibiti a birnin tarayyar Abuja 

Sarkin Musulmi mai murabus Alhaji Ibrahim Dasuki ya rasu a jiya da dare a Asibitin Nizzameye dake Abuja bayan doguwar rashin lafiya da yayi fama da ita.

Za a gudanar da jana’izarsa a Talata, 15 ga watan Nuwamba da karfe 2:00 na rana a Masallacin Sarkin Musulmi Muhammadu Bello dake garin Sokoto a jihar Sokoto a yankin Arewa maso yammacin kasar.
Allah ya jikansa da rahama. Ubangiji ya masa rahama, Amin.

Ku biyo shafinmu na Tuwita: @naijcomhausa

Tsohon Sarki da kuma Sarkin Musulmi mai murabus mai Ibrahim Dasuki da yaronsa Sambo Dasuki

Ibrahim Dasuki

The post Labari da dumi duminsa: Sarkin Musulmi mai murabus ya rasu (Hotuna) appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.




Moscow.media
Частные объявления сегодня





Rss.plus
















Музыкальные новости




























Спорт в России и мире

Новости спорта


Новости тенниса