Kudin fidda kai: Gwamnoni sun shiga uku
– An umurci Kwamitin majalisar dattawa akan jihohi da kananan hukumomi da su gudanar da bincike cikin yadda jihohi da kananan hukumomi suka kashe kudin fidda kan da aka basu
– Kwamtin ta aika wa gwamnan jihar Osun, Aregbesola cewa zasu zo gudanar da bincike a ranan 7 ga watan Disamba
– Zaku tuna cewa a shekaran da ya gabata, jihohin sun amshi kudi N713.7billion kudin fidda kai domin biyan albashin ma’aikatan jihohinsu
Da alamun cewa shugaba Buhari ya umurci majalisar dattawa da ta bincike gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola da wasu gwamnoni akan yadda suka kashe kudin fidda kan da gwamnatin tarayya ta basu domin biyan albashi.
Bukola Saraki ya aika kwamitin jihohi da kananan hukumomi da su je bincike jihar Osun Punch ta bada rahoto.
KU KARANTA: Muhimman abubuwan da suka wakana a jiya litinin
Kwamitin zata gudanar da bincike ne akan yadda gwamnatin Aregbesola ta kashe N34.988,900 da gwamnatin tarayya ta bata ta biya albashi.
A wata wasika da aka aikawa Aregbesola, shugaban kwamitin ya fadi masa cewa zasu kawo ziyara jihar ranan 7 ga watan Disamba domin binciken.
Zaku tuna cewa jihohi 23 un amshi kudin fidda kai daga hannun shugaba Buhari domin biyan albashin ma’aikatansu cikin 27 da suka nema.
Wata bincike da hukumar ICPC ta gudanar ya nuna cewa yawancin jihohin sun karkatar da kudin zuwa wasu abubuwa.
The post Kudin fidda kai: Gwamnoni sun shiga uku appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.