Boko Haram: Abubuwan ban mamaki 3 da Abubakar Shekau ya fada cikin sabon sako
Shugaban kungiyar Boko Haram; Abubakar Shekau ya kuma billowa, wannan karan a cikin wani sako ta faifan kaseti a kan YouTube.
Abubakar Shekau
Shekau ya maida martani ga sakon kasar Amurka da akayi a kwanan nan wanda Donald Trump ya lashe zabe a matsayin shugaban kasa mai jiran gado.
Karanta muhimman abubuwa guda uku da ya fada a cikin sakon a kasa:
KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa Dasuki ba zai halarci binne mahaifinsa ba
1. “Kada ku shagala da mutane irin Donald Trump da masu hadin gwiwa na duniya dake yakar yan uwanmu a Iraki, Syria, Afghanistan da kuma ko’ina.”
2. “Muna ci gaba da dogaro a kan addinimu kuma bazamu daina ba.”
3. “A bangarenmu yanzu aka fara yaki.”
Furucin Shekau na da ban mamaki saboda a yanzu ya daina samun goyon baya da karfin da ya ke samu a da daga kungiyar musulunci na Islamic State (ISIS) a watan Augusta.
A water Augusta kungiyar ISIS ta bayyana cewa ta maye gurbin Shekau da Abu Musab al-Barnawi, yaron wanda ya assasa kungiyar Boko Haram Mohammed Yusuf mai shekaru 22.
Duk da haka Shekau ya ki amincewa da nadin ya kuma bayyana cewa ISIS ta yaudare shi wanda ya amincewa a water Maris na shekara 2015.
The post Boko Haram: Abubuwan ban mamaki 3 da Abubakar Shekau ya fada cikin sabon sako appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.