Dasuki ya aika $40 million ga baffan Jonathan- Mai shaida
– Wani ma’aikacin Zenith Bank ya bayyana yadda Sambo Dasuki ya tura ma dan uwan Jonathan kudi
– Dan uwan Jonathan tare da uwargidansa na gurfana a gaban kotu a kan lafuka 7 na rashawa
Dasuki
Wani mai shaida Olabode Farinola, ya bayyana cewa Dambo Dasuki , tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara kan tsaro ya tura kudi $40 million (N12,589,454,800.00) zuwa asusun bankin dan uwan tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan , Azibaola Roberts,da uwargidansa.
KU KARANTA: Abun mamaki: Dasuki yayi watsi da mahaifinsa tsohon Sultan mai jinya a ranakunsa na karshe
Mai shaidan,wanda ma’aikacin Zenith Bank ne ya fada ma babban kotun tarayya karkashin alkalanci Jastis Nnamdi Dimgba cewa an tura kudin daga ofishin Sambo Dasuki zuwa wani kanfani OnePlus Holdings LTD.,na Mr. Roberts.
Game da cewara, Sambo Dasuki bai yi Magana akan cewa kudin da Zenith Bank ta tura kuskure bane.
“Ban san dalilin da yasa aka tura kudin ba kuma bamu samu wasika daga hannun Dasuki ba cewa kuskure mukayi,” Yace
Ana tuhumarsu ne da laifin karkatar da kudi $40 million (N12,589,454,800.00) na sayan kayan sadarwa ga jami’an tsaron Najeriya.
Ibrahim Mahe ,wani mai shaida, ya bayyana wa kotu cewa Sambo Dasuki ne kawai zai iya bayar da bayanin yadda aka turawa kamfanin OnePlus Holdings Limited $40 million (N12,589,454,800.00) na tsaro.
Amma, yaki fadawa kotun sunayen kmfanonin da suka amfana da da kudi. Jastis Dimgba ya dakatad da karan zuwa ranan 18 ga Nuwamba domin cigaba.
Ku biyo mu a shafin mu na Tuwita: @naijcomhausa
The post Dasuki ya aika $40 million ga baffan Jonathan- Mai shaida appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.