Osinbajo, Saraki, Dogara sun gana akan neman bashin $30bn
– Femi Adesina, yace hakikanin al’amarin shine bawai majalisa tayi watsi da bukatan bane
– Manyan shugabannin gwamnati sun gana ne a ofishin mataimakin shugaban kasa a fadar Aso Rock
Buhari and Osinbajo
Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, Shugaban majalisan dattawa, Bukola Saraki; kakakin majalisan wakilai, Yakuhu Dogara, sun gana.
Manyan shugabannin gwamnati sun gana ne a ofishin mataimakin shugaban kasa a fadar Aso Rock jiya litinin, 14 ga watan Nuwamba. Jaridar Dailypost ta bada rahoto.
KU KARANTA:Mu muka kashe Abu Ali, kuma kadan ma kenan-Shekau
Duk da cewan ba’a tabbatar da dalilin ganawar va. Ana kyautata zaton cewa sun gana ne domin tattaunawa akan rashin amincewan da majalisan dattawa tayi akan bashin $30bn da shugaba Muhammadu Buhari ya nema domin gudanar da aiki.
Amma, mai magana da yawun shugaban shugaban kasa, Femi Adesina, yace hakikanin al’amarin shine bawai majalisa tayi watsi da bukatan bane kuma zasu sake aikawa majalisa.
Adesina yace : “Zaku lura cewan majalisan dattawa tace tana bukatan bayanai filla filla ne,bawai tayi watsi da neman bashin bane.
“Wannan ba gwamnati maras hankali bane kuma kafin ta nukaci abu, tayi abinda ya kamata, amma idan majalisa ta nemi karin bayanai, sai muyi bayanin kuma mu sake turawa.”
Zaku tuna cewa wannan shine lokaci na 3 da shugaban majalisan dattawa, Bukola Saraki zai je fadar shugaban kasa a wannan marran yana ganawa da shugaba Buhari.
Ku biyo mu a shafinmu na Tuwita: @naijcomhausa
The post Osinbajo, Saraki, Dogara sun gana akan neman bashin $30bn appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.