Добавить новость
ru24.net
World News in Dutch
Ноябрь
2016

Shugaba Buhari ya isa kasar Morocco (Hotuna)

0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa babban birnin kasar Morocco, Marrakech da yammacin ranar Litinin 14 ga watan Nuwamba gabanin taron canjin yanayi (COP-22) da zai gudana a kasar.

Shugaba Buhari ya samu tarba daga Wakilin shugaban kasa tare da ministan kasashen waje da hadin kai a filin tashin jirage na Mogado.

Shugaba Buhari ya samu rakiyar ministan harkokin kasashen waje Geofrey Onyeama, Ministan kula da yanayi Amina Mohamed, shugaban kwamitin kula da yanayi na majalisar wakilai Samuel Onuigbo, shugaban kwamitin kula da yanayi na majalisar dattawa Bukar Abba Ibrahim, da takwararsa Sanata Oluremi Tinubu.

KU KARANTA: Lebura yayi ma matar Malam ciki

Shugaba Buhari zai halarci taron ne kasancewar Najeriya na cikin jerin kasashen da suka rattafa hannu kan daftarin kawo karshen matsalolin da canjin yanayi ke yi ma duniya gaba daya a birnin Marrakech, za’a fara taron daga 14-16 ga watan Nuwamba.

Shugaban zai halarci bikin bude taron, inda zai gabatar da kasida yayin babban taron tattaunawa na mahalarta. Sa’annan shugaban zai halarci taron bikin murnan zagayowar ranar Afirka wanda aka yi ma taken “tashi daga maganar fatar baki, zuwa aiki don bayar dagudunmuwa tare da tabbatar da shirin habbaka hanyoyin samar da wuta a Afirka”

Bugu da kari shugaba Buhari zai halarci taron shuwagabannin Afirka a yayin babban taron.

The post Shugaba Buhari ya isa kasar Morocco (Hotuna) appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.




Moscow.media
Частные объявления сегодня





Rss.plus
















Музыкальные новости




























Спорт в России и мире

Новости спорта


Новости тенниса