Добавить новость
ru24.net
World News in Dutch
Ноябрь
2016

Kwana 1 a Ofis: Karanta abin da Obaseki yayi ma baki

0

Sabon gwamnan jihar Edo Gwamna Godwin Obaseki ya fara aiki, inda ya shiga Ofis da misalin karfe 7:45 na safiyar ranar Litinin, 14 ga watan Nuwamba.

Gwamnan tare da mataimakinsa Philip Shaibu sun fara zagayen ayyukan dake gudana a jihar, awanni kadan da shigarsu Ofis.

Gwamna Obaseki da mukarrabansa

Da fari dai sai da Gwamna Obaseki ya saurari faretin girmamawa daga yansanda, inda daga bisani kuma ya wuce Ofishinsa. Jaridar The Nation ta bayar da rahoton cewar Gwamnan bai saurari tarin bakin da suka kawo masa ziyarar murna ba, sai dai kawai an hange shi tare da abokan aikinsa suna yin wata ganawa.

Yan siyasa da dama masu rige rigen zuwa taya shi murna sun sha mamaki, inda jami’an tsaro suka hana su zarya a fadar gwamnatin. Gwamna Obaseki ya gana da manyan sakatarorin ma’aikatun jihar, sa’annan yabi kadin takardun karbar ragamar mulki tare da mataimakinsa. Daga nan sai shugaba ma’aikatan jihar ya zagaya da shi gidan gwamnati.

KU KARANTA: Za’a kammala aikin hanyar Legas-Ibadan, inji Fashola

Hakazalika sabon gwamnan ya kai wata ziyara ga kwalejin kimiyya ta Bini don gane ma idonsa halin da kwalejin ke ciki. A cewar sa, zai cigaba da tafiyar da gwamnati da manyan sakatarori don sauya akalar mulki tare da rage tsadar mulki.

A ranar asabar 12 ga watan Nuwamba ne Obaseki ya karbi ragamar mulki daga hannun tsohon gwamna Adams Oshimole a filin wasa na Samuel Ogbemudia.

The post Kwana 1 a Ofis: Karanta abin da Obaseki yayi ma baki appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.




Moscow.media
Частные объявления сегодня





Rss.plus
















Музыкальные новости




























Спорт в России и мире

Новости спорта


Новости тенниса