Shin Donald Trump dan asalin kasar Amurka ne?
Gidan talabijin na News Channel ya fidda wasu shaidu na hotuna, wanda ya ke nuna cewa sabon zababben shugaban kasar Amurka Donald Trump ba haifaffen kasar Amurka ba ne.
Gidan talabijin na Neo channels na kasar Pakistan sun fidda hoton wani yaro wanda aka ce an dauka shekaru da dama da suka shude, lokacin da Donald Trump yaro a kasar Pakistan.
Gidan talabijin na News Channel sun dauki alhakin cewa Donald Trump wanda aka fi sani da kiyayya karara ga wadanda suka yi hijira suka dawo kasar Amurka, an haifa shi a shekara ta 1946, a garin Waziristan. Kuma sun fadi cewa ainahin sunan shi Dawood Ibrahim Khan.
Ku karanta kuma:- -mazan-ne-ya-kamata-su-kasance-kitchen-babangida.html.
Kamar yadda suka yi rohoto sunce Trump ya tashi a garin Waziristan na kasar Pakistan, kuma yayi karatun shi na firamare a can kafin wadanda ke rikon shi su dauke shi zuwa Amurka bayan iyayen shi sun mutu.
Rohoton da aka yada sati a mako kafin a sanar Trump yaci shugaban kasa cewa” Trump ba dan kasar Amurka bane haifaffen Pakistan ne.
Sun kuma kara bayyana cewa ba sune asalin wadanda suka samo labarin ba, sunce sun samu labarin daga twitter be, kuma sun samu caccaka kan saka labarin da yake bata suna.
The post Shin Donald Trump dan asalin kasar Amurka ne? appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.