Gwamnatin tarayya bazata bari Dasuki ya halarci binne mahaifinsa ba – umarni daga tarayya
Akwai alamu masu karfi dake nuna cewa tsohon mai ba shugaban kasa shawara a harkan tsaro Sambo Dasuki ba zai samu damar hallartan binne mahaifinsa da za’ayi a jihar Sakkwato ba.
Sambo Dasuki wanda hukumar yan sandan farar hula na DSS ta tsare kusan kimanin shekara daya kan zargin cin hanci da rashawa ya rasa mahaifinsa Alhaji Ibrahim Dasuki a jiya a Abuja.
Marigayi Ibrahim Dasuki
Mahaifin nasa mai rasuwa wanda ya kasance tsohon Sultan na Sakkwato wato sarkin musulmai mai murabus, ya mutu yana da shekara 93.
Bisa ga PRNigeria za’a binne Sultan din a yau Talata 15 ga watan Nuwamba, 2016 bayan sallar azahar da karfe 2 na rana a filin Hubbaren Shehu Usman Dan Fodio dake jihar Sakkwato.
KU KARANTA KUMA: Ya kamata maza ma su kasance a kitchen – Babangida Aliyu
gwamnatin tarayya ta tsare tsohon mai ba shugaban kasa shawara a harkan tsaro, Sambo Dasuki a ranar 1 ga watan Disamba, 2015 duk da bailin da manyan kotuna daban-daban suka bashi a Abuja. Kotun ECOWAS ma ta bada umarnin sakinsa.
Zuwa yanzu ba’a san ko gwamnati zata barshi zuwa don wani lokaci don ya yi duban karshe ga mahaifinsa a lokacin binne shi.
A halin yanzu, yan Najeriya sun nuna yardan sun a cewa Sambo Dasuki na fuskantar irin radadin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fuskanta a lokacin da yake shugaban kasa a mulkin soja.
Sambo Dasuki ne ya kama Buhari a lokacin da yake shugaban kasa a mulkin soja. An tsare shin a tsawon shekaru kuma ba’a bashi damar zuwa ganin gawar mahaifiyarsa da ta mutu ba.
A yau Buhari ya kasance shugaban kasa yayinda Sambo Dasuki ke tsare kuma ba zai halarci binne mahaifinsa ba.
The post Gwamnatin tarayya bazata bari Dasuki ya halarci binne mahaifinsa ba – umarni daga tarayya appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.