Muhimman abubuwan da suka wakana a jiya litinin
Jaridar NAIJ.com ta tattaro muku muhimman abubuwan da suka wakana a fadin kasa a jiya litinin,14 ga watan Nuwamba.
1. Duk da matsin tattalin arziki, yan majalisa sun siya motoci da N3.6bn
Jaridar Punch ta bada rahoton cewa, duk da halin matsin tattalin arzikin da najeriya ke ciki, majalisan dokokin najeriya ya biya kudin motoci 360 domin baiwa yan majalisan.
2. Labari mai ban tausai na matar da ta auri saurayinta mai kanjamau
Wata daliba mai karatun gaba da digiri na farko mai suna Talatu John (sunan karya) ta auri wani mutum mai suna Emmanuel wanda ya sa mata ciwon kanjamau. Sun fara soyayya bayan sun hadu a 2014.
3. ‘Yan Kasuwa kabilar Igbo dake Lagos sunyi alkawarin ci gaba da bada goyon baya
‘Yan kasuwa ‘yan kabilar Igbo dake Lagos sun ci alwashin ci gaba da goyon bayan ci gaban jihar, ta bukaci gwamnatin ta Kara yawan tuntubarsu domin kyakyawar fahimta.
4. An sake gano wasu kudade $175m dangane ga Patience Jonathan
Patience Jonathan and Ibrahim Magu
Uwargidan tsohon shugaban kasa , Patience Jonathan,ta shiga uku yayinda hukumar EFCC tayi bibitan wasu kudi $175m asusun ta. Matsala daya shine an gano cewan an cire kudin daga asusun ba tare da sanin wanda ya cire ba.
5. Buhari ya bada umurnin sallaman ma’aikatan gwamnati
An samu rahotannin cewa Gwamnatin tarayya tana shirin koran ma’aikata a hukumomin da ke karkashin ma’aikatar sufurin jirgin sama.
6. Wike dan baranda ne, ba gwamna ba – Amaechi
Ministan Sufuri,Rotimi Amaechi yayi kira da magoya bayan APC kada su ja baya bisa ga barazanar Wike a zaben da za’a gabatar a jihar ribas da za’a gudanar a ranan 10 ga Disamba.
7. Najeriya zata fara fitar da Shinkafa kasar waje – Ogbeh
Ministan aikin noma, Cif Udu Ogbeh ya bayyana cewa Najeriya takusa ta fara fitar da shinkafa mai kyau zuwa kasar waje da sairan sassan duniya.
8. Dalilin daya sa Donald Trump ya kada ni – Hillary Clinton
‘Yar takarar shugaban kasa kalkashin inuwar jam’iyyar Democratic Hillary Clinton ta dora laifin kasheta da Donald Trump yayi a zaben ranar Talata kan daraktan hukumar binciken laifuffuka (FBI) James Comey.
Ku biyo mu a shafinmu ta Tuwita: @naijhausacom
The post Muhimman abubuwan da suka wakana a jiya litinin appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.