Добавить новость
ru24.net
World News in Dutch
Ноябрь
2016

Shugaban Kasa yayi murabus

0

– Firayim Minista na Kasar Jamhuriyyar Congo yayi murabus daga kan mulki

 BBC tace Augustin Matata na Congo ya sauka daga kan mulki da kuma wannan na cikin tsarin yarjejeniya da aka yi da ‘yan adawa

 

 

 

 

 

 

 

Gidan BBC ta rahoto cewa Firayim Ministan Kasar Jamhuriyyar Congo yayi murabus daga kan mulki. Firayim Minista Augustin Matata yayi murabus din domin ya ba ‘yan hamayya damar kafa Gwamnati a Kasar ta Jamhuriyyar Congo.

Firayim Minista Matata ya sauka daga matsayin na sa ne a matsayin cika alkawarin yarjejeniyar da aka yi tsakanin ‘Yan adawa da Gwamnatin Kasar. Ana dai kokarin kawo karshen rikicin siyasar da ta barke a Kasar ta Congo. Hakan ma zai sa a dage zaben Shugaban Kasar zuwa shekaru biyu masu zuwa.

KU KARANTA: Ban taba sata ba-Atiku Abubakar

Mutane da dama a Kasar dai suna ta zanga-zanga, suka ce ba su yarda da dage zaben ba. Masu zanga-zangan sun zargi Shugaban Kasar Joseph Kabila da kokarin cigaba da zama a mulki. A da dai an shirya yin zaben ne wata mai zuwa.

A Kasar Kenya kuwa wani abun al’ajabi ya faru inda wasu iyaye suka saka wa dan suka haifa sunan sabon Shugaban Kasar Amurka, Donald Trump. Wadannan iyaye sun yi wa sabon Shugaban Kasar Amurka Donald Trump takawara saboda tsabar soyayya. Wannan abu dai ya kawo ce-ce-ku-ce a Kasar ta Kenya.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

 

The post Shugaban Kasa yayi murabus appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.




Moscow.media
Частные объявления сегодня





Rss.plus
















Музыкальные новости




























Спорт в России и мире

Новости спорта


Новости тенниса