Добавить новость
ru24.net
World News in Dutch
Ноябрь
2016

Za a fuskanci matsanaciyar yunwa shekarar 2017

0

– Idan ba a dauki mataki ba, ‘yan Najeriya za su shiga wani mummunan hali na matsanaciyar yunwa badi

 Mai magana da bakin Shugaban Kasar, Garba Shehu yayi wannan bayani a wani Gidan Rediyo

– Kasar Najeriya ta fi kowa noman hatsi a kaf fadin Afrika, sai dai

 

 

 

 

 

 

Mai magana da yawun-bakin Shugaban Kasa Muhammadu Buhai, Malam Garba Shehu ya bayyanawa ‘Yan Najeriya cewa da yiwuwar Kasar ta fuskaci matsanaciyar yunwa zuwa farkon shekara mai zuwa. Mai ba Shugaban Kasar shawara a game da harkar yada labarai yayi wannan bayani ne a jiya a Gidan Rediyon Freedom da ke Kano.

Mai ba Shugaban Kasa Buhari shawara a game da harkar yada labarai yace ana da bukatar hatsi a kasuwannin duniya, wanda kuma zai kara kamari. Hakan ta sa wasu ‘Yan Najeriya ke fitar da abinci zuwa Kasashen waje. Garba Shehu yace idan ba a dauki mataki ba, Najeriya za ta rasa abin da za ta ci shekara mai zuwa.

KU KARANTA: Mu muka kashe Soja-Shekau

Kasar Najeriya ta fi kowace Kasa a fadin Nahiyar Afrika noman hatsi, an kuma yi dace an samu damina mai albarka. Sai dai kuma saboda yanayin yadda ake neman hatsin a wasu wurare, ‘Yan Kasar suna fitar da abinci zuwa ketare, hakan na iya janyo matsanaciyar yunwa a Kasar.

Ministan noma, Audu Ogbeh ya koka da wannan lamari. Yanzu haka Kasashe har irin su Brazil suna neman shinkafa daga Najeriya. Garba Shehu yace ana iya fama da matsanaciyar yunwa badi.

 

The post Za a fuskanci matsanaciyar yunwa shekarar 2017 appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.




Moscow.media
Частные объявления сегодня





Rss.plus
















Музыкальные новости




























Спорт в России и мире

Новости спорта


Новости тенниса