Добавить новость
ru24.net
World News in Dutch
Ноябрь
2016

Gwamnoni sun hura wuta sunsa Buhari ya mika wuya

0

Osinbajo yayi taron da aka kira “na keke da keke” tare da Bukola Saraki,Dogara

An samu labarin cewa daga yanzu dole. ne a tuntubi gwamnoni da shuwagabannin All Progressive Congress (APC) kafin shugaba Muhammad Buhari yayi wani nadin mukami.

Sabuwar manufa: Kamar yadda manufar ta tanada, jiya shugaban ya umurci mataimakinsa Yemi Osinbajo daya yi taro da masu ruwa da tsaki masu fada aji game da  nadin mambobin hukumomin gwamnati.

KU KARANTA: Canji: Yan Najeriya sun bukaci Buhari yayi koyi da Ganduje

Osinbajo yayi taron da aka kira “na keke da keke” tare da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara, sakataren gwamnatin tarayya (SGF) Babachir Lawal,shugaban gamayyar gwamnonin Najeriya (NGF) Abdulaziz Yari, shugaban gamayyar gwamnonin APC Rochas Okorocha da kuma wakilan gwamnonin daga shiyyoyi shidda na kasar.

Amma mambobin shugaban na bayan fage wadanda ake Kira “cabal” a turance sun bukaci a basu kashi 40 na guraben. Mambobin na bayan fage sunce shugaban ke bukatar guraben, amma gwamnoni sunce Buhari ya gaya masu ba zai tsoma bakinsa cikin aikinsu ba.

Wata majiya wada ta halarci taron na cewa shugaban ya fada ma gwamnonin cewa yayi mamaki matuka adawar data biyo  bayan nadin jakadu  da aka yi.

Adawar gwamnoni: Gwamnonin sun fada ma Buhari adawarsu cewa kwamitin zaben bai tuntubesu ba, kuma basu san wadanda aka zaba ba. Majiyar na cewa wadanda shugaban yaba alhakin samo masa wadanda suka iya aiki sun dauko yaransu ne.

Domin kauce ma “aringizon nade-nade” a cewar majiyar, shugaban kasa ya tabbatar ma gwamnonin da shugabannin jam’iyya cewa daga yanzu zai rika tuntubar gwamnoni, majalisar tarayya da kuma shugabannin jam’iyya kan nade-nade.

Majiyar ta cigaba da cewa “shugaban yayi watsi da masu nadi na bayan fage wadanda suka sashi yaji kunya kan nade-naden sirri. Yanzu za’a rika tuntuba kafin nade-nade”

 

The post Gwamnoni sun hura wuta sunsa Buhari ya mika wuya appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.




Moscow.media
Частные объявления сегодня





Rss.plus
















Музыкальные новости




























Спорт в России и мире

Новости спорта


Новости тенниса