Добавить новость
ru24.net
World News in Dutch
Ноябрь
2016

Ka ji abin da wasu suka yi wa Donald Trump?

0

– Wasu iyaye sun saka wa ‘dan su da suka haifa suna Donald Trump

– Mahaifin yaron yace yana matukar kaunar sabon shugaban Kasar Amurka da kuma wannan abu ya faru ne a kasar Kenya

 

 

 

 

 

 

A Kasar Kenya wani abun al’ajabi ya faru inda wasu iyaye suka saka wa dan suka haifa sunan sabon Shugaban Kasar Amurka, Donald Trump. Wadannan iyaye sun yi sabon Shugaban Kasar Amurka Donald Trump takawara saboda tsabar soyayya.

Jaridar Daily Nation ta Kasar Kenya ta rahoto wannan labara. Iyayen wannan yaro sun ce Donald Trump yana matukar burge su. Mahaifin wannan ‘da yace shi musamman akidu da manufafofin wannan mutumi watau Donald Trump yana ba sa sha’awa kwarai da gaske.

KU KARANTA: Za a saki Nnamdi Kanu

Mista Felix Otiano ya sakawa dan sa da haifa kwanaki dai suna Donald Trump. An sakawa wannan yaro sunan Donald Trump ne tun ma kafin takwarar na sa ya san zai lashe zaben Shugaban  Kasar Amurka. Mista Felix, Mahaifin wannan ‘da yace Donald Trump ya cancanci zama Shugaban Kasar Amuka.

Wannan abu dai ya kawo ce-ce-ku-ce a Kasar, shi dai mahaifin yace ba don ya zama Shugaban Kasa ya masa takwara da dan cikin sa ba. Kwanakin baya, Farfesa Wole Soyinka yace Najeriya da sauran Kasashen Afrika ba za su rika samun irin taimakon da suka rika samu a lokacin Shugaba Barrack Obama ba tun da Donald Trump ya zama sabon Shugaban Kasar Amurka.

 

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

 

 

The post Ka ji abin da wasu suka yi wa Donald Trump? appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.




Moscow.media
Частные объявления сегодня





Rss.plus
















Музыкальные новости




























Спорт в России и мире

Новости спорта


Новости тенниса