Amurka Ta Sanya Ma Shuwagabannin Boko Haram Guda 2 Takunkumi
Ma’ajiyar Amurka Ta bayyana cewa an sanya ma Muhammad Nur, wanda ya wakilci Boko Haram a lokacin da sanyawa da gwamnatin Najeriya takunkumi saboda ta’addanci, kunar bakin wake da kuma harin da aka kaima ofishin majalisar dinkin duniya dake Najeriya a 2012.
Yan ta’addan Boko Haram
Suka ce: “Nur yana goyan bayan Boko Haram, kuma yana yaki da gwamnatin tarayyar Najeriya. Na biyun kuma shine Nustafa Chadi, wanda a 2013 ya jagoranci Boko Haram ya kai hari a Chad. ”
Wanna yazo be bayan da Amurka ta lissafi Boko Haram a cikin kungiyoyin ta’addanci na duniya. Manufar yin hakan shine a kulle su daga hanyoyin kudade na duniya.
Ma’ajin ta Anurka tace @Boko Haram ta tashi daga sace yan mata izuwa kai hare-hare. Ta zama matsala ga dukkan al’umma.
A shekarar data wuce, majalisar tsaro ta majalisar dinkin duniya at lissafi Abubakar Shekau a matsayin dan ta’adda. Sannan kuma aka lissafi Boko Haram a matsayin wani sashe na kungiyar AlQaeda ta kasashen Larabawa da Bakar Fata.
The post Amurka Ta Sanya Ma Shuwagabannin Boko Haram Guda 2 Takunkumi appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.