Saraki Ya Musanta Zargin Da Sahara Reporters Tayi Mashi
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki ya musanta zargin da Jaridar Sahara Reporters tayi mashi cewa yana da hannu wajen sace kudaden sawo makamai wanda Sambo Dasuki ya fidda.
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki
Amma jami’i mai hudda da jama’a na shugaban majalisar dattawan, Yusuph Olaniyonu, ya musanta zargin inda ya bayyana cewa Bukola Saraki bai taba yin aiki da Wata hukuma ko kwamiti mai alaka da tsaron kasa ba.
Yace: “A matsayin na mamba na majalisar dattawa, ban taba aiki a wani kwamitin tsaro ba. Hasali ma dai nine shugaban adawa da gwamnatin GoodluckwJonathan. Ta yaya za’a ce na samu damar da zani ci fuskanta wani.
“Shugaban majalisa yana so ya sanar da mutane cewa kokarin da Sahara Reporters take yi da masu ingizata shine su cire no daga Ofishin shugaban majalisar dattawa. Wannan wani abu ne wanda suka kasa yi a cikin majalisa.”
Sannan kuma ya bayyana cewa wannan shine karo na 3 wanda Sahara Reporters take yi mashi kazafi. Sannan ya bayyana cewa bata fi karfin doka ba duk da cewa ba a Najeriya take ba.
The post Saraki Ya Musanta Zargin Da Sahara Reporters Tayi Mashi appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.